Maganin kuraje pimples da habbatisauda

 

Domin magance matsalar kurajen fuska wanda ake cema pimples.

Zaa samo garin habbatisauda sai ahada da man simsim sai kuma ahada shi da garin alkama cokali daya, sai ashafa a fuska idan zaa kwanta, da safe kuma sai awanke fuska da ruwan dumi, da kuma sabulu, malam mutum zai cigaba da yin wannan har zuwa Sati daya.

 

Malam yace kash inama da ace bayan haka kuma kasamo zait habbatil baraka kana zubawa kadan acikin wani nauin abin shanka mai sanyi. Insha ALLAH dakayi mamaki.

 

MAGANIN KURAJEN FUSKA 

 

Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza.

Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.

Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya.

Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.

Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska.

Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.

A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya.

Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne..

· A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.

· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo.

Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.

· A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

· a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

· A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi

 

Yadda za a magance tabo da kurajen
fuska...
.
Matsalar kuraje da tabon fuska sun
fi shafar matasa, mata da maza.
Wani lokaci sai an sha wahalar
magance kurajen fuska, amma sai
tabo ya ki bacewa.
.
Rashin bacewar
tabo a fuska na bata kwalliya. Sau da
yawa za a ga ba a son shiga taron
mutane domin wadannan tabon.
.
Da yawan mutane sun gwada
mayukan kantin, domin rabuwa da
tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu
kuma ba su yi sa’a ba.
.
A yau mun zo da bayanin yadda za a
magance tabon fuska. Muna son a
san cewa daya za a zaba daga cikin
hanyoyin da muka lissafo, kada a
hada su gaba daya. Domin yin hakan
zai kara lahanta fuska ne.
.
A samu ganyen dogonyaro, sai a
hada shi da kurkum, sannan sai a
shafa a fuska. A jira tsawon minti 15,
sannan a wanke da ruwan dumi.
· Za a iya shafa markadadden
dankalin Turawa a kan tabo. Hakan
na magance kurajen fuska, sannan ya
hana su sake fitowa.
.
Ko a daka tafarnuwa sai a shafa a kan
tabo. Tafarnuwa tana wari, amma
tana gyara fuska, sannan ta magance
tabon fuska.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top