Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda sun kama mawakin ne a ranar Talata, 6 ga watan Agusta, inda ba tare da wata wata ba suka zarce dashi zuwa ofishin Yansanda masu gudanar da binciken manyan laifuka domin amsa tambayoyi.
Yansanda sun bayyana cewa sun kama Tekno ne saboda laifin bayyana yan mata tsirara, tare da yawo dasu cikin bainar jama’a a kan titunan jahar Legas, wanda hakan ya saba ma doka, kamar yadda kaakakin rundunar ya bayyana.
A makon data gabata ne aka hangi Tekno yana yawo da wasu yan mata cikin wani akwati mai haske da mota ke janye da shi wanda ana iya hangen cikinsa, inda yan matan suke rawar batsa tsirara, yayin da shi kuma yake musu likin kudi, a daidai gadar Lekki da Ikoyi.
Wannan fitsara ta yi matukar bata ma jama’an Legas rai, wanda hakan ya janyo korafi da babban murya daga sassan jama’a daban daban, daga ciki har da gwamnatin jahar Legas, wanda ta yi tir da wannan rashin tarbiyya da girmama mutuncin jama’a.
Sai dai a cewar mawakin, yayi amfani da motar ne wajen safarar yan matan, abokan aikinsa da kuma kayan aiki zuwa wani waje da zasu dauki bidiyon waka, amma sai motar ta lalace musu a hanya, daga bisani kuma ya nemi afwa.
Kaakakin Yansandan jahar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da kama Tekno tare da yan matan biyu da suke aikata wannan badala, sa’annan yace sn kaddamar da bincike, kuma zasu gurfanar dashi gaban kotu idan hali ya yi.
Tuni ita ma hukumar kula da tallace tallace na jahar Legas ta dakatar da kamfanin da ta dauki nauyin wannan fitsara da mawakin ya yi, watau Pro-Vision Media Systems Limited.
Majiyarmu ta samu wannan labari ne daga legithausa
©HausaLoaded
Post a Comment