Me Ake Nufi Da Tsabta?
Tsabta na nufin kawar da duk wani abu da ya shafi kazanta da gyara yadda ya dace na jiki ,muhalli da kuma cikin unguwanni da ma gari bakidaya. Wannan Karon zan yi magana ne akan tsabtar jiki ganin yadda ke taka muhimmiyar rawa cikin rayuwar ma’aurata musamman mata.
Tabbas rashin tsabtar jiki babbar matsala ce ga ‘ya mace budurwa ko matar aure wanda zai iya haifar mata da koma baya cikin rayuwarta bakidaya. Abin kunya ce da takaici ga duk macen da ta rasa tsabtar jiki, mata da yawa kan zauna ba tare da tsabtace jiki ba har sai maigida ya kai ga yin magana ko in ya Karo aure a lokacin zaki ga an fara gyarawa wannan ba daidai ba ne.
Tsabta cikon addini ne kuma jigo ne da ke jan ragamar rayuwar aure bakidaya.
Wadanne Irin Matsaloli Rashin Tsabtar Jiki Ke Haifarwa?
Rashin tsabtar jiki na jawo matsaloli masu tarin yawa kadan daga cikinsu :
1: Maigida ya fara bibiyar matan banza.
2: Yana jawo raini a wurin maigida da ma wadanda zama ya hadaki da sure.
3: Yana jawo yara ma su tashi da shi har gidajen auren su.
4: yana haddasa tsana da gaba ga maaurata.
5: yana haifarwa mace wata cutar dabam.
6: yana jawo yawaitar mace -macen aure.
7: yana jawowa maigida aure aure.
Ta Ya Ya Za Mu Gyara?
Zamu iya gyarawa ta hanyoyi kamar haka:
1: kar ki ba da duk wata kofa da maigida zai fahimci kazantarki.
2: ki sa ni duk in da ‘ya mace ta ke ‘yar gyara da tsabtace.
3: yi kokari ki zama (role model) abin koyi ga yaranki da ma mutanen da kike zaune a cikinsu.
4: ki tsabtace gashin kanki ta hanyar wankewa da yin kitso akai akai ki bi shi da turarukan gashi.
5: fuskarki kar ki barta da kuraje yi kokari ki magance su a duk lkcn da suka fito.
6: ki gyara faratunki (nails) ki kawata yatsun da lalle,.
7: Tsabtace cikin baki da kawata lebe (lips) da Man baki don hanashi tsatssagewa.
8: karki bar kafarki da kaushi ko faso.
9: In da duk ke tsirad da gashi yi kokari kiga kina shabing lokaci zuwa lokaci.
10: Duk wani lungu da sako da ke jikinki yi kokari kiga kin tsabtashi tare da bi da turaruka masu sanyin kamshi.
SHAWARA GA MATA.
1: karki ba wa maigida kofar da zai Kalli wata mace tsabta saboda ke kin gaza ta wannan bangaren.
2: ki sa ni tsabtar jiki kan kara dankon soyayya tsakanin ma’aurata.
3:ki kasance a kodayaushe cikin Kamshi.
4: karki bari maigida ya kafa hujjar karo aure saboda rashin tsabtar jikinki.
5: ki sa ni tsabtar jikin ki kan jawo maigida ya daukeki tamkar sarauniya.
6: ki sa ni sai da tsabtar jiki ado da kwalliya ke tasiri. A duk lokacin da za ki kasance cikin tsabta da gyaran jiki zaki kasance tamkar amarya a kodayaushe wurin maigida.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment