Masana lafiyar fata sun bayyana cewa yin wanka a kulli yana baiwa jikin ‘dan adam matsala.

Majiyarmu ta binciko wani bincike da Likitocin kula da lafiyar fata na duniyar suka gudanar akan illar yin wanka kullin.

Likitocin sun bayyana cewa “Illar yin wanka a kullin yafi amfanin yin wankan a kulli yaumin saboda illar da yake haifar wa fatar jikin mutum.”

“Muna yin wankan da ya wuce gona da iri. Amma yana da kyau mu gane cewa muna yin hakan ne kawai saboda wasu abubuwan yau da kullin, ko kuma saboda iyaye da kafafin labarai suna fada mana haka domin tseratar da jikinmu daga yin wari.” – Dakta Ranella Hirsch.

“Sai dai gaskiyar magana, wanka sau daya a rana ma yana tsotsar da ruwan jiki tare da cire sinadaren maiko a jikinmu.”

“Jikin dan adam yana fitar da wasu sinadaran maiko wadanda suke taimakawa wajen rike ruwan jikin domin tafiyar da aikace-aikacen sassan jiki ba tare da wata tangarda ba.”

“Irin wannan sinadarin masu wanka a kullin suke rasa wa.”

“Iya adadin da mutum yake wanka, shine iya adadin asarar wasu nau’o’in kwayoyi masu amfani a jiki wanda hakan yana kai wa ga samun cutar fata.”

Dakta Elaine Larson ta Jami’ar Columbia, Dakta C Brandon Mitchell na Jami’ar George ta Washington dake kasar Amurka da sauran likitoci sun tabbatar da binciken.

Daga karshe binciken ya tabbatar da cewa yin wanka na kasa da minti 10 a duk bayan kwanaki 2 zuwa 3 shine abinda fatar ‘dan adam tafi so.

Sai dai a bangaren Dakta Mitchell, ya bayyana cewa yin wanka sau daya ko sau biyu a cikin mako shine abinda yafi dacewa ga dukkanin mutane. -Kamar yacce binciken majiyarmu ya tabbatar.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top