Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar, a ranar Alhamis, 8/8/2019 ya kaddamar da rabon kudaden layya ga marayun dake  gundumomi 86 dake fadin jihar Sokoto ga uwayen kasar.

Sarkin Musulmi,ya yabawa Gwamnatin jihar na daurewa da wannan shirin.

Sarkin Musulmi ya kuma jinjinawa Hukumar karba da raba Zakka ko wakafi ta jihar Sokoto, akan kokarin kwatantawa da dagewa ga wannan aikin, kuma ya yi kira ga Sarakunan da aka baiwa wannan amanar da su sani duk wanda ya ci hakkin maraya to yaci wuta, kuma  majalisar ba za ta lamunce ba.

Tun daga farko, sai da Shugaban zartarwa na Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki,Sadaukin Sakwwato ya ce gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da kashe kudi Naira miliyan Goma Sha Bakwai da dubu Dari biyu , domin sayen shanu na layya ga yara marayu da tsoffin da ba su da hali dake  fadin gundumomi 86 da ke  kananin hukumomin jihar 23.

Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ce kasafin kudin zasu kasance kowace gunduma zasu karfi Naira dubu dari da hamsin, domin sayen maraki da naira dubu Goma,na aikin gyaran naman da wasu naira dubu goma domin zirga-zirga ga 'yan kwamitin, jumla kowace gunduma za ta amshi naira dubu dari da Saba'in (170,000:00).

Sadaukin Sakkwato,Ya kuma yabawa gwamnatin jihar akan wannan kokarin tare da yabawa majalisar Sarkin musulmi akan goyon baya da shawarwarin da take baiwa Hukumar, ya kuma sanar ba iyayen kasar da kada su sanya siyasa a cikin wannan Lamarin, Ya sanar cewa za su nada kananin Kwamitocin da za su zagaya domin ganin yadda aka yi da wannan amanar ta hakkin marayun.

Daga bisani mai Alfarma Sarkin  musulmi ya kaddamar da shirin a fadar sa dake Sokoto.
Shide wannan shirin na yin Layya ga yara maras iyaye da tsofaffi, yana tasiri sosai na kuranyewa wadannan Yaran da ba su da galihu da kuranye masu damuwar rashin yin layya da sanya masu farin ciki a ranar sallah.

Muna  fatar Allah ya biyar duk mai hannu a ciki. Hukumar Zakka DA Wakafi #sozecom #layyargwamnatinjiharsokotogamarayudamabukata #sokotostatezakatandendomentcommissionannualdisbusmentlayya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top