Lokacin da mace ko namiji suke cikin fishi suna yiwa juna magana mara dadi, kowa yana kokarin ya bada nasa uzurin, a lokacin duk basu sanin yadda maganar ke cutar da abokin zaman ba, in mace ko namiji naso su fadawa abokin zamansu matsalar dasuke basu zasu iya amfani da rubuta wasika sai ajiye inda za a gani, sabida shi rubutu a takarda koda lafazan marasa dadi ne bazasu kai zafin in masoyi ya fadesu da baki ba haka mai karantawar zai karanta cikin tsanaki da nazari akan abin ba tare da musayar maganganu ba. Wasika tana kare masoya daga fada da musu a tsakaninsu musamman in lafizan bamasu dadi bane sosai. A fara rubuta wasikar da haushi ko bakin cikin da akeji sai a gama karshen da lafazi na soyayya ko yaya ne. Ayi rubutu mara yawa kuma a yaren da za a gane a iya karantawa.

A al adar mace bata tamabayar abu daga gun masoyinta, tafiso yayi mata dakansa ba sai ta tambaya ba, a aladar namiji kuma sai antambayeshi yake yin abu. In mace tana bukatar wani abu a gun namiji sai ta tambaya zata samu, macen dabata iya tamabayar abu sai tafara da abubuwan da namiji yake mata ba tare da ta tambaya ba, sai tana tamabayarsa tunda yasaba yi mata itama zata saba tambayar abinda takeso,tana tambayar abinda bayasanyi dan ta saba da jin aa, sannan tana yi masa godiya inyace eh.

Mace tanabin wannan hanyoyi wajen tambayar abu. 

1. Ta tambaya alokacin daya kamata. Kar sai zaiyi miki abu kiyi sauri ki tambaya.

2. Kartanasa dole akan abinda ta tambaya.

3. Kartayi tsayi ko kwana kwana.

Akarshe ina mai rokon duk wanda ya karanta ko ya amfani wannan rubutu nawa da ya yadashi ga yan uwa dansu amfana, kar aji kunyar bawa baba ko mama sabida wanna zai iya kawomana gyara sosai a zamantakewarmu.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top