Wasu manyan jaruman Kannywood da suka hada da Ali Nuhu, Usman Uzee da Maryam Booth sun zama wakilan kamfanin sufuri na CarXie. Jaruman sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da wakilcin ne tare da wakilan kamfanin da ranar Juma'a a Legas. Kamar kamfanin Uber da Taxify, CarXie kamfanin sufuri ne na Najeriya da ke aiki a jihohin Najeriya da suka hada Legas, Abuja, Kaduna, Kano Awka da Enugu.


 "Wannan sabon tsari ne daga kungiyar DuKAN, kwararen kamfanin fasaha na Najeriya. Kamfanin sufurin zai fadada ayyukansa zuwa wasu jihohin Najeriya," inji daya daga cikin sabbin wakilan kamfanin, Uzee. Jaruman uku sune mutane ne farko da kamfanin ya dauka a matsayin wakilansa.

 A hirar da tayi da Premium Times, Booth ta ce "Na rattaba hannu a kan kwangiloli guda biyu a wannan shekarar, daya da Airtel sannan na biyun da Ajinomoto. Ga kuma wannan na sake samu." Booth kuma ta ce za tayi bidiyon tallata kamfanonin. "Zan kuma yi amfani da kafafen sada zumunta na wurin tallata hajojinsu da wasu abubuwan."

 Masoya, da 'yan uwa da abokan arzikin jaruman sun rika taya mu murnar samun wannan cigaban ta shafinsu na Instagram.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top