Wani likita dake aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin Ismail Adigun ya bayyana cewa mai fama da gyambon ciki, wato ‘Ulsa’ zai iya yin azumin Ramadan cikin sauki idan ya nisanta kansa daga abincin da ka iya tado radadin cutar.

Alamun wannan cutar sun hada amai, ciwon ciki, rashin cikin mutum iya nika abinci yadda ya kamata, ciwon kirji da sauran su.

Hanyoyin guje wa tada cutar a lokacin Ramadan.

1. Da zaran an yi bude baki mutum ya gaggauta cin dabino. Hakan na taimakawawa mai dauke da cutar.

2. A guji cin abincin da aka soya ko kuma abincin dake da mai dayawa.

3. A guji shan abubuwa masu tsami kamar su kunun tsamiya, kunun zaki, koko, lemu, lemun tsami da sauran su.

4. Za a iya shan madaran da aka dama da ruwan sanyi ko kuma da ruwan zafi a lokacin da za a yi sahur domin hana cutar tasowa.

5. Za a iya shan ruwan kwakwa.

6. A rika gauraya abinci da ganyayyaki, kamar su kabeji, Latas da sauransu.

7. Kamata ya yi mai dauke da wannan cuta ya ci abinci kadan-kadan bayan an sharuwa.

8. A guji cin abinci dake da yaji.

9. A guji cin abinci mai nauyi.

10. A tanaji maganin rage radadin Ulsa din a kusa.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top