GAREKU MATA MASU HANKALI....®
Baki buqatar perfect guy kafin kiyi aure, kawai Kina buqatar Gayen da zaki aminta dashi ne, wanda zai nunawa duniya ke tashi ce. Amma idan kika kuskura kika fara bude kafafunki ga Gaye, toh ki tabbatar baki daga cikin matan daya dace ya aura. Kisan matsayinki a wajen Gaye, ki daina daukan matsayin matar aure alhali kuwa bakiyi auren ba budurwa kawai kike ga Gaye.

Ba kowane Namiji bane dakika hadu dashi yakeda genuine interest a kanki. Abun bakin ciki gareku mata shine kuna ganin kunada abinda zaku iya canja xuciyar namiji dashi, wanda sam ba haka bane.

Babu macen da zata canja xuciyar namiji, namiji shi zai canjane saboda yana buqatar canjawan. Idan har namiji yana qaunar ki, bazaiyi wasan saurayi da budurwa dake ba wanda ba aure kuma zaiji tsoron rasaki. Yar'uwa ki daina 6ata lokacin ki bisa tunanin wai zaki sanya namiji ya aminta dake har ya aureki alhali ke kuwa Kina zubar da qimarki.

Kada ki kuskura jikinki yazamto fansa wajen neman mijin aure, ki tsare jikinki har sai bayan aure.

Wassu abubuwan da zaki kiyaye domin sanya namiji ya aminta dake:

1. Kada kiyi qarya domin namiji ya soki, domin da zarar gaskiya ta bayyana, zai maisheki wawiya.

2. Kada ki nuna ke ta Allah ne idan kinsan ba haka kike ba wai domin saurayi ya soki, idan halinki na asali ya bayyana, zakiji kunya.

3. Kada kiyi amfani da kudi wajen soyayyan namiji, domin daga kudin sun daina Shigowa, zasu sanya ciwo a zucuyarki.

4. Kada ki kuskura kice idan Kika bari Gaye ya miki ciki zaisa dole ya aureki, hakan ba komai zai maisheki ba face Uwar da batayi aure ba.

5. Kada ki Kuskura ki dauka zaki sanya Gaye ya aminta dake ta hanyar bude mishi kafa, wallahi yana gajiya dake zai kiraki mai arha, ya gujeki ya nemo wata.

6. Tara samari dayawa bashi ke nuna kyakkyawa ce ke ba, kaya mai arha shikeda customers dayawa.

7. Looking too expensive abune mai kyau, amma hakan zai kori matasa dayawa daga xuwa gareki.
Daga karshe, idan kindamu kisani, aure Kamar layin markade ne, idan kina layi markadenki bai zo ba, kada ki gajiya saboda layinki na zuwa. Ko yaushe zauna cikin shiri domin Kina daf da shiga sabuwar rayuwa.
Ya Ubangiji wadanda ke layin markade Ka rabasu da sharrin tsinkewar belt kona dauke wutan lantarki, wadanda suka markada kuma Ya Allah Ka basu ikon cigaba da shan miya mai dadi.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top