Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun sace daya daga cikin fitattun Daraktocin fina-finan hausa na Kannywood, Salihu Mua’zu a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Jos daga jihar Kaduna, yayinda suka bukaci Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansansa.

Yayansa Alhaji Sani Mu’azu ya bayyana cewar, an tare su ne a kauyen Saya a kusa da Jingir da ke karamar hukumar Bassa ta Jihar Plateau, kuma yau da safe Yan bindigar sun tuntube su, inda suke neman diyyar naira miliyan 10.

Yayan nasa ya bukaci al'ummar Najeriya da su yi wa dan uwansa addu'a domin samun kubuta daga hannun 'yan bindigar.

Idan ba a manta ba, Salihu Mu’azu ne ya jagoranci sasanta rikici tsakanin fitattun jaruman Kannywood wato Ali Nuhu da Adam Zango.

Sata da garkuwa da jama'a domin karbar kudin fansa na ci gaba da zama babban annubar da ke addabar jihohin arewacin Najeriya a 'yan kwanakin nan.
RFIhausa.

Post a Comment

 
Top