A yau idan ka ce za ka yi Aure daga ranar da ka fara fafutuka Neman Abun Auren zuwa ranar Aurenka in ba kai wasa ba sai wando ya daina zama a qugunka,

 saboda tsadar Auren, tun daga kan sadaki kayan lefe da kudin gaisuwar uwa da uba da sauran su.

Wannan ya sa samari da dama suka kasa yin aure.
Amma a yau idan ka yi niyyar yin zini a rana daya (in dai za ka iya yi) da mata 20 ko sama da haka za ka iya yi.

 Sannan kuma kudin da za ka kashe ba zai taka kara ba ballantana ya karya shi ba. Kai wasu ma ko sisi ba sa kashewa, kyauta sukeyi saboda yan matan gasu nan kamar jamfa a Jos, 

kuma suna bukatar auren amma samari ba kudi, iyaye kuma sai mugun son Abun duniya su dai burinsu yarsu ta Auri me kudi

Wannan ya sa aka taru aka hada karfi da karfe tsakanin samari da yan mata da kuma iyaye ake ta sabawa Allah babu qaqqatawa,

cikin abubuwan da za su kawo karshen zinace-zinace shi ne farashin aure ya fado kasa warwas!, 

Domin babban abun
bukata a aure shi ne sadaki, shi ma
idan babu shi ana iya badawa bashi, duk fa Musulunci ya yi haka ne domin a rage fasadi a doron kasa

Amma duk da Haka Wasu wawaye suna ganin Rashin Yin Auren kamar shine dai-dai

A haqiqanin gaskiya tun da na tashi ban taba gani ko jin labarin An daura aure bashi ba. Kai hasalima kowacce shekara farashin aure qara tashi sama yake kamar gwauran zabo.

Sai dai nasan farashin sadaki yana yin tsada ne bisa dalilin talauci da ake fama da shi. Sakamakon wasu iyayen suna karawa kudin yawa ne domin suyi wa yarsu kayan daki dan a fita kunya.

Ita kuma kunya ana so a fice ta ne a gurin yan gutsiri-tsoma, wadanda idan ba a yi wa yarinya kayan a zo a gani ba za su bi unguwa suna gulmace-gulmace, karshe ya koma gori wajen amarya da iyayenta.

Wannan yasa iyaye ke tsauwala kudin sadaki da abubuwa makamanta wannan.

To amma, sai suka manta cewa ita
kunya ta Ubangiji ake gudu, ba ta
wani ba.

Domin idan diyarka tayi cikin shege a gidanka sai ka fi kowa jin kunya a duniya, kuma wannan shi ne abin kunya da ake gudu, amma ba kunyar kayan lefe ko sadaki ba.

Allah ya sa mu dace.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top