Mun samu labari yanzun nan daga kotun kolin Najeriya inda akayi zama ta karshe kan zaben gwamnan jihar Zamfara.

A halin da ake cikin yanzu, kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar All Progressives Congress APC ba tada hakkin takara a zaben gwamnan jihar kuma saboda haka, an yi fatali da dukkan kuri'un da ta samu.
Ida al'amari ya zama haka, jam'iyyar da ta zo na biyu a zaben da dan takararta za'a nada matsayin gwamnan jihar ranar 29 ga watan mayu, 2019.

Gamayyar alkalai biyar na kotun sun yi ittifaki a ranar Juma'a cewa jam'iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga ka'idojin jam'iyyar.
Babban alkali, Paul Adamu Galinji, ya ce dukkan kuri'un da aka kadawa jam'iyyar APC banza ne kuma an jam'iyyar da tazo na biyu a zabubbukan ne zababbun masu kujerar.
Kana kotun ta bada umurnin baiwa Sanata Kabiru Marafa kudi milyan goma saboda rashin adalcin da akayi musu.

Alkalai sun ja kunnen yan siyasan Najeriya kan kokarin lalata demokradiyyan kasar.

Source: Legit.ng

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top