Daraktan kamfanin shirya fina-finan Hausa kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Falalu Dorayi, yayi kira ga yan Arewa da su hadu, su kafa kungiyar sa kai sannan su kare kansu daga ayyukan yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar. Falalu yayi wannan kiran ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu. Da yake martani akan kashe-kashen yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara, Falalu yayi bayanin cew ya zama dole yan arewa su kafa kwamitoci da za su kafa yan sa kai kamar yadda mutanen Borno suka yi wa Boko Haram.
“Maganar Tashin hankula da suke Faruwa a wasu YANKUNA na arewa, sai fa mun tashi daga bacci mun hadu wajan nemawa kanmu mafita kafin gwamnati tazo da tata mafitar. “Sau tari kafin gwamnati ta kawo dauki ko agajin tsaro an gama galabaita, tilas muyi (kwamati) na kare garuruwanmu daga mahara, kamar yadda a kai a BORNO (Civilian JTF).
"Ko dan mutuncin MATANMU, ‘YAYANMU da DUKIYOYINMU. Lallai wannan dole akan ko wanne Yanki na arewa domin zaman jiran sai an kawo dauki to cigaban MATSALAR NE, hakan kuma wallhi barazana ne ga zaman LAFIYA.
“Kullum sai kaji Labarin an shiga gari a kashe wasu ko an dauke su domin a biya fansa a karbesu. Duk mai kyakkyawan tunani yasan matsala tana farawa kadan-kadan in aka gaza daukar mataki har tazo ta gagari GWAMMATI da al'umma. Mun gani a MAIDUGURI.
“Ya Allah! Ka kawo karshen wannan masifa da take faruwa a KATSINA da ZAMFARA da wasu Yankuna na AREWA. "Masu tada fitinar ko su waye Allah ka rusa Aniyarsu. Allah ka bamu zaman lafiya, Allah ka tona asirin duk wanda yake da hannu a wannan mummunan aiki. Ya Allah! Ka sanya kasarmu Nigeria cikin aminci da zama lafiya.”
Sources: Instagram
©HausaLoaded
Post a Comment