Wai me ya sa hakuri idan an yi miki kishiya yake da wahala ko da kuwa an gaya miki kafin ayo ta? A da tunanina kamar kowace mace shi ne muddan miji ya ce zai kara aure, to tabbas ya dena son matarsa. Amma sai ya kasance cewa ko a ta biyu kika zo kishin yana nan dai. Na dauka tunda ke aka auro a matsayin amarya ba za ki ji wani kishi ba dan ya ce ze karo wata. Ashe ko ke ce ta hudu kin san an rufe kofa kishin nan dai yana nan. Toh ashe kenan ta ko yaya kika kalli abun, dole dai kishin nan yana tare da mu.

Sai kwanan nan ba da dadewa ba na gano wata dabara, wanda ina kyautata zaton da izinin Allah in kika yi amfani da shi za ki samu sauki kuma za ki ci riba. Allah ya bani ikon iya yin bayanin shi yadda za a iya ganewa.


Abu na farko da na gane shi ne: Yana da kyau tun yanzu ki zauna ki auna ki gani kuma ki tambayi kanki shin mijina yana so na kuwa? Wannan ita ce tambaya ta farko kuma wanda ya fi kowanne mahimmanci saboda dukkanin mu ‘Ya yan Adam, wato maza da mata gaba daya, masamman a cikin aure, abun da kawai muke so mu sani, mu tabbatar, kuma mu yadda da shi kenan domin samun farin ciki da kwanciyan hankali. Cewa aboki ko abokiyar zamana tana ko yana so na. Ki duba rayuwarku tunda kuka yi aure har izuwa yanzu ki gani kuma ki tambayi kanki tambayoyi kamar haka:

1) Shin a duk shekarun nan da muka yi da bawan Allahn nan yaya yake treating (kula da sha’anina)?

2) Yana kyautata mun, yana kula da hakkokina, yana kula da hakkin yara, yana kokarin faranta mun, yana girmama ni da daraja iyaye na dayan’uwana?

3) A duk shekarun nan da muka yi ya taba yin miki wani abu na rashin mutunci ko na cin zarafi?

Ki yi kokari ki amsa wadnnan tambayoyin fisabilliah cikin adalci. Idan kika amsa su kuma kika gamsu cewa eh kin yi imani da Allah mijin ki yana sonki sai abu na gaba.

Daman can dukkanninmu mun sani cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya fada mana a cikin Alkur’ani cewa ya basu daman auren sama da mace daya kuma ya ba zuciyarsu daman son matan nan duka duk da dai sai an samu wacce zuciyar sa za ta fi so, amma Allah ya ce kar ya nuna a fili ya bar shi a cikin ziciyar sa. Toh ashe kenan eh da gaske dan ya ce zai yi aure ba wai ya dena sonki ba ne. A;a, dama Allah yaba zuciyar sa damar iya son mace sama da daya.

Abu Na Biyu:

Tun da har kin amsa tambayoyin nan kin yi mishi adalci kuma kin tabbatar cewa yana son ki. Toh a koda yaushe sai ki dauka ke din ya fi so. Don ko tambayan shi kika yi haka za ce miki. Kuma yana da kyau ki yarda da duk abin da ya fada miki saboda duk bincikenki ba za ki iya taba ganin cikin zuciyarsa ba. Abu mafi sauki mafi maslaha shi ne ki yarda da amsar da ya baki.
Kashi 70% na maza ko da sun kara aure babu abin da yake canzawa a gidan matar shi ko kadan. Amma duk da haka sai ki ga matar taki ta kwantar da hankalinta taci ribar zama da shi. Wani a lokacin ne ma zai fi kyautata mata da yi mata abubuwan da za su sa hankalinta ya kwanta amma duk da haka sai ki bada hadin kai da dama a zauna lafiya.

Idan har kika tabbatar mijinki yana sonki, toh a lokacin da zai kara aure in kina da wayo da hikima har sai kin fi morarsa. Za ki iya kafa mishi sharudda kuma ki fadi abubuwan da sai an yi miki kafin a yi auren, wallahi zai yi. Saboda burinsa a wannan lokacin shi ne kwanciyar hankalinki. Idan kika bashi hadin kai toh, wallahi sai ya zamo kamar ma bautarki yake yi. Dan babu wani abu da za’a taba yi sai da izininki.

Ke ce za ki zamo megidan da uwargidan duk a lokaci guda. Idan har za mu dinga ma mazajenmu adalci wajen aunawa mu gani tsakani da Allah, wallahi yawanci za mu gane cewa suna son mu kuma dan za su kara aure ba dalili ba ne na tashin hankali da hana mishi da kanki zaman lafiya.

A Karshe…
Ya kamata ki yi kokari ki gane tun yanzu kuma ki sani cewa a kowani lokaci zancen kara aure zai iya tasowa amma ba zai hana ki sakewa ki ji dadin aurenki ba. A lokacin ma ya kamata ki kara son mijinki kuma ki bashi hadin kai. Wallahi zai mika miki wuka da nama sai yadda kika yi.

Allah Ubangiji ya cigaba da dafa mana duniya da lahira baki daya in sha Allah, ya sa muna daga cikin masu babban rabo fid dunya wal akhira.

Taku, Binta Shehu Bamalli 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top