Ban da Saurin Fushi: Ita mace bambancinta da namiji tana da saurin tasirantuwa ne da lamari, abu kadan zai iya sa wa ta so abu ko ta ki shi, kamar yadda karamin abu zai iya bakanta mata rai ko ya sauko da ita bayan ta fusata, tana da saurin daukar zafi kuma cike take da hakuri da saurin yafiya, wadannan siffofin ne ma suka sa ake iya rayuwa da ita na tsawon lokaci, kai namiji bai kamata a ce ka dauki wasu ‘yan siffofinta ba, masamman saurin fushi da karancin duba abin da zai kai ya komo nan gaba, ita duk abin da ya gamsar da zuciyarta an gama, kai kana da bukatar aiki da kwakwalwa wajen duba sakamakon abu in har ka sami kanka a ciki.

Misali mace tana matukar kaunarka za ta iya tsittsine maka ta uwa ta uba ta tsaya kan sai ka sake ta, in ka jure ka hakura, ka kau da kanka za ta dawo tana ba ka hakuri da guntun hawayenta da komai kan cewa sharrin shedan ne, in kuma ka biye mata za ka sake ta karshe za ku yi nadama ku biyu din. Ya kamata in har ta nuna maka nummunan halinta, to kai a tuna alkhairinta, ka diba hidimar da take maka, bugu da kari ga ma wata zuriya da ta daure ku da ita gaba daya, ka kalli abin da zai biyo baya in ka rabu da ita.

Ka bar Ruko: Wasu abubuwan da dama mace kan yi su ne don zolaya ba da gaske take yi ba, ko don yanayin halittar da Allah ya yi mata, misali: Za ka zaunar da ita ne ka yi mata lissafin duk matsalolin da kake da su, da yanayin yadda ka sami kanka, amma kana matsawa sai ka ga kamar ba da ita kuka yi maganar ba, nan take za ta ce maka “Ba mu da kaza da kaza fa” ba wai ta karyata ka ba ne ko maganar ka ba ta dame ta ba, gani take wadannan abubuwan da ta gaya maka tabbas akwai bukatarsu a gida, kuma in har ba ta gaya maka ba za ka iya yin fushi ka ce ba ta fada ba, shi ya sa kawai ta yanke wannan hukuncin.

To ka yi mu’amala da ita a yadda take kawai banda ruko, kar in ta yi maka laifi ka rika karanto mata wasu laifuffuka da ta yi a baya, wadanda tuni ta ma manta da su ba ta tunanin su. In ta yi abu ta roke ka cewa, ka yi hakuri, to ka daure ka hakura din bayan nuna mata laifinta, amma ka sani mace ba halittar namiji ne da ita ba za ta maimaita ba. Ka tuna kai namiji ne ita kuma mace ce, duk wani aikin karfi da maza ke yi mace in ta tsaya za ta yi, ta ma fi namijin, amma banda sha’anin zuciya, anan rauninsu yake. Don haka sai mu dunga hakuri da su.

Kar Ka Rika Yi Wa Matarka Gori: In dai mace ce, ka yi abin da ya zama wajibi a kanka kawai, ka dauka cewa duk abin da kake mata ba don ita kake yi ba, da farko dai don Allah ne, na biyu kuma kana son ka gyara gidanka ne, in har za ka rika ba iyalinka abu kana dubawa nan gaba har gori za ka rika yi, cewa “Ashe ban yi miki kaza da kaza ba?” Hakan kuma ba dabi’ar namiji ba ce, ka yi abin da ya dace kawai, ka nuna kaunarka kare ta, za ta ji dadi ta dage wajen kyautata maka ita ma.

To bare kuma komai ka yi wa iyalinka, duk da cewa hakkinta ne a kanka sai ka yi, Allah kuma zai ba ka lada a kai, wani hadisi da Buhari da Muslim suka rawaito Annabi SAW yana cewa “Ba wani abu da za ka ba wa iyakinka wanda kake neman fuskar Allah da shi sai an ba ka ladarsa, har lomar da za ka saka a bakin matarka” ban sani ba ko shi ne na ga Larabawa suna yanko loma su sa a bakin matansu, ko ka taba gwadawa? Ya kamata mu guji yi wa matarmu gori a kan abin da muke yi musu a matsayinmu na mazajansu.

Ina bai wa mazajen aure shawara a kan su dunga hakori da matayensu da Allah ya mallaka musu. Lalle duk wanda ya sauke nauyin hidimar iyalinsa, to Allah zai taimake shi cikin wannan rayuwar duniya da lahira. Namiji yana da hankalin da mace ba ta da shi, mu zama masu bai wa matarmu uzuri a kan halittar da Allah ya yi musu.

Yana da kyau ma’aurata su san halayyar junansu ta hanyar da babu yaudara, karya, ko cuwa-cuwa. Ya kasance ma’aurata sun fahimci hanyar da za su iya sulhunta kansu ba tare da wani mutum na uku ya shigo tsakaninsu ba, hakan na samuwa ne ta irin yadda kowannensu ya fahimci matsayinsa a zamansu na ma’aurata. Miji ya sani cewa ragamar tafiyar da gida a kansa yake. Idan aka fahimci wadannan shawarwari, to in Allah ya yadda za a samu kyakykyawan zamantakewar aure.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top