Har yanzu tattaunawarmu zai cigaba ne a kan zuwan azumi, kasancewar ma’aurata kan manta da yin wani tanadi don taryar azumi, sai ta yadda za a canza Kayan kitchen,canza abinci na alfarma, wasu har da canjin Kayan furniture’s. Duk wadannan ba laifi ba ne, sai dai yana da kyau mu fahimci irin mutanen da ke kewaye da mu musamman mu mata.
Uwargida a tanadinta na farko ya zamto ta san cewar ibada take yi, sai me za ta samar wa makota da bayin Allah a lokacin buda baki? Me zata mika a masallacin unguwarsu a lokacin buda baki a matsayin neman lada? Marayu nawa za ta tallafawa wurin abinci da Kayan sallah? Maimakon canjin Kayan kitchen masu tsada uwargida ta bawa maigida shawara a lokacin wannan sayyayar da sayan tabarmai, butoci da sauransu a massalacin unguwarsu.A duk lokacin da Kika tanadi wani abu Kama na abinci ko abin amfani to ki tuna da wadanda ke kewaye dake abinda ya da ce ki basu.
‘Yan uwa mata mu yi tanadin abubuwan alheri a cikin wata me alfarma dake tunkararmu. Mu bawa mazaje shawara wurin aikata aikin alheri. Wasu mata da yawa ,basa damuwa da bukatar wani matukar su tasu bukatar ta biya, mu canza dabi’un mu a wannan lokaci.
Wasu kan yi yunkurin kashe aurensu a saboda maigida bai iya yi musu abin da suka bukata ba, ko su kashe auren ma bakidaya. To mu sa ni girke girke, ko sauya Kayan gida ba su ne abin da ake bukata ba a cikin watan azumi.Abin bukata shi ne Yaya za a yi in samu lada me tarin yawa?
Iyaye mata kada mu ba da kofar da ganin hidimar gidan wata ya jawo mana matsala a gidajen aurenmu, domin darajarki dakin mijinki.
Allah ya sa mu gyara.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment