Kamar yadda muka dauko bayani dalla-dalla a kan yadda za ki yi wa maigida tarbiya ya zamo me halaye da dabi’u irin wadanda kike so, sannan kuma ke ma ki samu yadda kike so in sha Allah, toh za mu cigaba.


Idan uwargida na biye da ni, kuma Allah ya sa kin fahimci dukkannin bayanin da ya gabata, kuma kin yi nasara har Allah ya sa kin ga canji a tare da megida. 

Abu na gaba shi ne ke kuma se ki shigo da irin abubuwan da kike so. Amma kafin nan yana da mahimmanci a ce kin gane kuma kin fahimci yanayin megida. Saboda idan kika fahimci yanayin shi, toh ke da kanki za ki san lokacin da ya kamata ki dinga shigar da bukatarki.

In dai ba akwai wata matsala ko damuwa ba, yawanci wadannan lokutan guda uku lokuta ne na shigar da bukatar ki cikin wasa da dariya.

1. Lokacin da ya shirya tsaf zai fita daga gida
2. Lokacin da yeke cin abinci
3. Lokacin kwanciyar barci

Kafin ki fara shigar da bukatunki (in kina biye da ni, ba bukata ta kudi ko makamancin haka muke magana a nan ba, muna magana ne a kan irin abubuwa na soyayya da tareraya da kike sha’awa megida ya dinga yi miki domin karin nishadi, kwanciyar hankali da natsuwa).

A lokacin da kika tashi sanar da megida abubuwan da kike so kar ki tsaya bashi aiki, ma’ana kar ki fito mishi da bukatar ki ta hanyar kacici-kacici ki barshi da cinka. 

Ki fito fili ki fada mishi abin da kike so dalla-dalla kuma yadda ze gane. Saboda yawancin lokuta mu mata se mu isar da sako ko bukatarmu a dunkule ba tare da mun bayyana shi yadda wanda muke magana da shi ze gane ba. Saboda haka in kin fada mishi, cikin murya me dadi se ki tambaye shi idan ya fahimci abin da kike nufi, idan ya gane falillahil hamd, idan ya ce be gane ba se ki sake yi mishi bayani yadda ze gane. Ki yi hakuri, ki daure har se ya fahimta cikin wasa da dariya.


Yana iya yiwuwa a ranar farko da kika bayyana bukatarki, ki yi sa’a megida ya fara miki su a ranar, wannan yana da nasaba da jin dadin irin ababen da kike yi mishi wanda ya sauya mishi yanayin rayuwarsa gaba daya. Kuma yana iya yiwu cewa se bayan wani dan lokaci sannan za ki samu. Ba wai saboda ba ya jin dadin abubuwan da kikeyi ba, se dai saboda mutane kala-kala ne kuma wasu se a hankali suke aiwatar da canji. Idan ya kasance haka, to ki zamo me hakuri, kar da ki karaya, sannu a hankali in kika daure in sha Allah za ki samu yadda kike so.

Toh, uwar gida, da yardar Allah in kika zamo me hakuri kuma me lura , sannu a hankali rayuwarku za ta canja, za ku zamo ma’abota jin dadi, nishadi, kwanciyar hankali da natsuwa a cikin rayuwarku. Wannan shi ne dan takaitacciyar dabara da za ki iya amfani da ita domin ki taimaka muku ku samu yadda kuke so in Sha Allah.

Ina fata Allah Ubangiji ya cigaba da dafa mana duniya da lahira baki daya. Ina fata Allah Ubangiji ya warware mana dukkannin wata matsala ko damuwa da ta addabi al’umma alfarman Manzo Sallallahu alaihi wa Sallam, alfarmar wannan wata me albarka. Allahumma ameen ya Allah.

Taku,
Binta Shehu Bamalli


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top