Mustapha Badamasi Naburaska ya yafe wa takwarar sa Hadiza Aliyu Gabon karar da ya kai ta gaban kotu bayan da ta durkusa gwiwoyi kasa ta roke shi a harabar kotu a yau Litinin.

Bayanan da LEADERSHIP A YAU ta samu sun tabbatar da cewa, jami’an ‘yan sanda sun kamo jarumar ne a Kaduna bayan da kotun majistare da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin damko ta sakamakon kin amsa gayyatar kotun da ta yi.

A zaman kotun na yau, lauyan Hadiza Gabon ya shigar da roko ga kotu ne kan ta janye shari’ar tunda dai an samu sasanta wa tsakanin wadanda su ke rikicin kuma ta roke shi, ya yafe ma ta.

Daga nan sai Mai shari’a Muntari Dandago ya ja kunnen jarumar a kan kin amsa gayyatar kotu da ta yi, ya na mai cewa, babu wani mutum a Najeriya da ya fi karfin kotu ta gayyace shi, ballantana ita.

Ya bada misalin cewa, shugaban majalisar dattawa na kasa da babban sufeton ‘yan sanda da makamantansu ma sun amsa gayyatar kotuna daban-daban.

Daga nan sai ya yanke hukuncin cewa, nan da shekara guda idan a ka kara jin ta ko ganin ta ta yi ko harara ga Jarumi Naburaska, to kotu za ta kamo ta kuma ta hukunta ta.

Idan dai za a iya tunawa, Naburaska ya shigar da karar ne bisa zargin cin zarafin sa da kuma barazana ga rayuwar sa da jarumar ta yi a kwanakin baya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top