(ya zama ezna ga wasu 'yan matan) 

~ Qawata '' kinga irin kayan da Ahmed yakawo min kuwa? hmmmm.. ai ina sanar miki ya gama fitar dani kunya,ga kayan azumi ga kuma dinkunan sallah,ni yanzu sallah kawai nake jira lokaci yayi.

~ Tayi shiru da alaman ranta yana bace, ke! wai meyake damunki ne? mtsssss.. taja dogon tsaki,kyaleni maimuna da wancan matsiyacin nan.
kina ganin Azumi har yayi nisa ,babu abinda yakawo min balle ma nasa rai da dinkin sallah.

~ Tayi salati game da zaro ido ke' kar dai kice min Harisu bai kawo miki komai ba?
'' eh babu abinda ya kawomin,sai wani zancen banza wai baida kudi nayi hakuri''.

~ Tab wallahi ! Jamila karki yarda wannan ai jawo wa kai raini ne,sannu a hankali tayi ta zugata game da mata hudubar shaidan,da sannu kuwa duk maganganun suka shiga cikin kunnuwanta.

Dare misalin karfe 8:00pm

~ Ranki ya dade ina ta magana kin kyale ni,laifin menayi ne?

~ Ta kallesa,kallon wulakanci '' taja dogon tsaki,kaga bafa zaiyuwu ba nagaya maka matukar bazakamin kayan azumi da dinkin sallah ba,to wallahi ina gaya maka karshen zamanmu yayi.;

~ Cikin tashin hankali yace, haba jamila don Allah kiyi hakuri kinsan ina miki wallahi bani da kudi ne,ga hidimar kannena kina ganin nine komai a gidanmu,wallahi inda ina da hali ba sai ma kin tambaye ni za.......

~ A fusace ta katse sa,'' dakata mallam bani da lokacin jin wannan banzan maganar a bakin ka,nagaya maka bazan ji kunya ba duk kawayena an masu,nan kanwata ma an kawo mata sai ni,to wallahi bazai yiwu ba sam bazan amince ba.

~ Kallon ta kawai yakeyi cike da mamakinta,yadda ta rufe ido akan abinda baizamu dole ba.
 ''iyakar kokarinsa yayi
   a lokacin don ya rarrashe ta,akan zai mata koda nan da bayan sallah ne amma taki sauraron sa ,karshe ma tafiya tayi ta barsa cike da takaicin ta''

~ Mahaifinta yayi kokarin ya mata dinki kala daya daidai karfin sa,amma zuciyar Jamila cike da dogon buri da kwadayi da kuma rashin godiya ga Allah,anata tunanin tafi karfin ace sallah itace dayin dinki kala daya bayan wasu kawayen ta data gani har da masu kala biyar ma.

~ Sanadin haka tasa kanta ta kowane hali sai fa tasamu karin kaya da kuma ankawo mata kayan azumi domin ta nunawa kawayen ta itama.

~ Tana cikin wannan halin ne ta hadu da wani shaidanin saurayi,lura da ita mace ce mai kwadayi da wannan damar yayi amfani ya mata dadin baki da kalaman yaudara ,ya nuna mata kudi akan matukar ta bashi kanta gobe zaizo ya dauke ta suje kasuwa ta zabi duk abinda take bukata.
 '' shaidaniyar zuciya
    makwadaiciya nan
     take ta amsa mishi
      cewa idan dare 
       yayi zata zo ''
tayi masa sallama, yayinda yabita da kallo hade da murmushin mugunta.

~ Da daddare ta shirya wa mahaifiyarta karya.
akan abin duniya ta sallama masa budurcinta😭😭.
ya mata dadin baki akan gobe ta shirya yana zuwa su fita.
ko kadan a lokacin zuciyarta babu wani nadamar abinda ta aikata sai ma ta matso goben tayi har ta fara lissafin abubuwan da zata dauka.lokacin da harisu ya fado mata a rai taja tsaki tana kara jin haushin sa.

 TO FA!

~ Washegari ,tana zaman jiransa shiru babu shi babu labarin sa,''ta kira numbernshi yana ringing amma yaki dauka a lokacin hankalinta ya fara tashi,koda taje gunsa nunawa yayi ma sam shi baigane ta ba karshe ma korar wulakanci yayi mata''.

~ Ta dawo gida cike da bakin ciki abinda ya faru,duk yadda taso samun abun bata samu ba,karshe dole dai da wannan kala dayan tayi sallah.

 WATA SABUWA....

~ Cikin kankanin lokaci yanayin ta yafara canzawa,ita ce kasala,tashin zuciya ,fuskantar yanayin datake ciki yasa hankalin mahaifiyar ta tashi.bata dai yanke hukunci ba ta dauke ta sukaje asibiti.

~ Gwajin farko doctor ya sanar mata tana dauke da juna biyu,daga ita har mahaifiyar nata kuka suka sa a tare,cikin tashin hankali ta shake ta tana tambayarta waye yayi mata cikin nan?tamkar wanda zata kashe ta dakyar doctorn yaraba su yana bawa mahaifiyar ta hakuri.

~ Koda suka dawo gida,da duka ta kara rufe ta tana kuka,tana fadin kin cucd ni jamila,kin jawo min abin kunya .

~ Lokacin da Jamila tasha azaba ta fadi sunan sa,koda suka je a banza domin cewa yayi kazafi ta masa shi baima san ta ba,bai taba ganin ta ba (kalu bale gare ku hakan yake faruwa duk lokacin days gama dake cewa zai yi baima san kiba kece dai aka bari da damuwa da tashin hankali)

~ Tsananin bakin ciki yasa mahaifinta yankar jiki ya fadi,nan take yasamu mutuwar barin jiki.

~ Magana bata boya nan unguwa ta dauka Jamila tayi cikin shege,ya zama daidai da kofar gida bata isa ta fita ba,rayuwa tayi mata kunci ,ta zamu cikin nadama .
tana dama rayuwarta na baya zai dawo da bata aikata abinda tayi ba,data tsaya matsayin da Allah ya ajiye ta da bata bi son zuciya ba da duk hakan bata faru ba.

 Abinda nake so ku fahimta a wannan guntun labarin dana kawo muku,wanda nake son yazamu ezna ga masu tunani da irin halayyan Jamila.
ga dai abinda ya faru da ita .
babu wani amfanin tsayawa rokon saurayi ya miki abu,ko daura masa nauyi wannan babban zubar da kima ce a gun mace.
abinda iyayen ki suka miki ki gode masu.
tun kafin ki girma baki zamu mutum ba iyayenki ke miki hidima ko lokacin da kuka hadu da saurayin naki ai ba tsirara ya ganki ba,don haka ina rokonki ki zama macen kwarai kar kwadayi da ganin ido yasa ki zubar da mutunci a titi.
domin dai kwadayi mabudin wahala ne.

Allah ya shirya damu kan tafarkin gaskiya ya ganar da wadanda suka kauce wa hanya.
Allah yasa muna daga cikin yantattun bayin da za'a gafarta masu a cikin watan Ramadan


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top