Masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood ya dauki zafi a yankwanai biyun da suka abata yayinda fusatattun mambobin kungiyar mawaka na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka zargi daraktan mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, Dauda Kahutu Rarara da wasu bakwai da yin sama da fadi a kudaden kungiyar da aka samu ta hanyar tallafi.

Fusatattun mambobin kungiyar a wani kwamitin mutum 11 karkashi n jagorancin mataimakin Shugaban kungiyar, Murtala Mamsa kuma Shugaban kungiyar reshen Abuja, tare da Ahmed Turaki Kaka a matsayin sakatare sun gayyaci Rarara wanda ya kasance Shugaban kungiyar, da wasu bakwai domin su gurfaa a gaban kwamitin bincike don wanke kansu daga zarge-zargen da ake masu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kafa kwamitin mutum 11 ne a makon da ya gabata lokacin da shugabannin kungiyar na jihohin arewa 19 suka yi wata ganawa mai muhimmanci a Jos.

A wata wasika wanda sakataren kwamitin, Ahmed Turaki ya rubuta yace akwai bukatar yin biciken saboda yawan korafe-korafe daga mambobin kungiyar kan zargin almubazaranci da kudade da aka tattara daga jama’a domin kaddamar da ayyuka daban-daban, kama daa tallafawa mambobin kungiyar zuwa siyan kayayyakin amfani na ofis da kuma siyan ababen hawa na kungiyar.

Wasikar ya kuma bayyana cewa duk da kudade da aka tattara domin aiwatar da wannan abubuwa babu abunda aka yi.

Wadanda aka tura ma wasikar gayyata sun hada da tsoho Shugaban kungiyar Haruna Aliyu Ningi, mukaddashin shuaban kuniyar na kasa, Haruna Baban Chinedu, Ibrahim Yala, Isiyaku Forest, Alfazazee, Kamilu Koko da kuma Baba Yanmedi.



Sai dai kakakin Rarara, Aminu Afandaj yace basu da masaniya akan wasikar.

A nashi bangaren kuma, Baba Chinedu ya tabbatar da samun wasikar sannan yace zai amsa gayyatar domin bai da guntun kasha a tsuliyarsa.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top