...to ga jerin wasu manyan ayyuka da Buhari ya yi a yankin Arewa

1. Aikin hanya mafi tsawo kuma mafi girma a Nijeriya da gwamnatin Buhari take yi a Arewa ne, yana da nisan sama da kilometer dari 450, shine daga Kano, Zaria, Kaduna zuwa Abuja.

2. Aikin tashar wutar Lantarki mafi girma a tarihin Nijeriya da gwamnatin shugaba Buhari take yi a Arewa ne, shine Manbilla hydro power station, idan an kammala zai samar da wuta megawatts dubu 3050.

3. Aikin bincike da hako man fetir Bauchi da Maiduguri, duk Arewa ne.

4. Tashar jiragen ruwa na farko a tarihin Arewa shugaba Buhari ne, itace Baro sea port, jihar Niger.

5. Aikin hanyar Kano zuwa Katsina, Arewa ne.

6. Hanyar Kano, Bauchi, Potiskum, har Borno, Arewa ne.

7. An mayar da filin jirgin saman Malam Aminu Kano terminal, irin na kasashen Turai, duk a gwamnatin Buhari, kuma Arewa.

8. Aikin hanyar Bye pass na Kano, Buhari ne, kuma Arewa ne.

9. An gina Army University a Biu jihar Borno har an fara karatu, Buhari ne, Arewa ne.

10. Ya kammala aikin tashar samar da wutan Lantarki na Kashimbila, jihar Taraba, Arewa ne.

11. Yana gina tashar wutan Lantarki da aka watsar da aiki shekaru 29 a Zungeru jihar Niger, yanzu an kai kashi 78 na kammalawa, Buhari ne, Arewa ne.

12. Ya kammala jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, Buhari ne, kuma Arewa ne.

13. Ciyar da yara 'yan primary a jigohin Nigeria, Arewa sun fi yawa, Buhari ne, Arewa ne.

14. Ya gina Air Force base mai girma, har da babban Asibitin sojojin a Bauchi, Buhari ne, Arewa ne.

15. Shirin N-power, Buhari ne, shugabar shirin 'yar Arewa ce.

16. Shugaban sojojin sama, kasa, Police, DSS, NYSC, FERMA, NITDA, duk ‘Yan Arewa Buhari ya bayar.

17. Tallafin noma da gwamnatin take bayarwa kashi 76 wa Arewa ne, Buhari ne Arewa ne.

18. Ministan tsaro, Ministar kudi, Ministan ilimi, duk Arewa ne.

19. Aikin Titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano ana kan yi, Buhari ne, Arewa ne.

20. Ginin Commodity market, Gezawa jihar Kano, Buhari ne, Arewa ne.

21. Ya gina Police Academy secondary school, a Kafin Madaki, jihar Bauchi  nan gaba kadan za'a kaddamar dashi, Buhari ne, Arewa ne.

22. Naira biliyan 60 wa jihar Kano dan samar da ruwan sha da aikin Dam-dam a jihar, Buhari ne, Arewa ne.(my home town)

23. Aikin hanyar Ganye, Mayo Belwa, zuwa Toungo cikin jihar Adamawa, Titin mai tsawon kilometer 112, an kusan kammalawa, Buhari ne, Arewa ne.

24. Ya kammala titin Kwantagora ta jihar Niger har zuwa cikin garin Yauri ta jihar Kebbi. Yanzu kuma aiki ya zarce daga Yauri zuwa Birnin Kebbi duk cikin jihar Kebbi, Buhari ne kuma a Arewa ne.

25. An yi nisa sosai aikin titin Jebba zuwa garin Ilorin jihar Kwara.

Dan haka idan mai magana Wawa ne, masu jin sa da sauraren sa garau suke ba wawaye bane, har yanzu ba'a kawo dalilin da zai sa mu yi adawa da Buhari ba tukun.

An gaushe ka Muhammad Buhari.

Daga shafin Kano ta Arewa Ina Mafita?

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top