SHIN MANZON ALLAH (S.A.W) YASAN GAIBU?

Prof. Ibrahim Maqari. Limamin masallacin kasa dake abuja (Chief imam national mosque) - Nigeria


Prof. Yace Adai duba littafin da kyau tukun kafin ace wai ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) bai san gaibu ba

Prof. Ibrahim Maqary yace idan mutum yace maka ANNABI S.A.W bai san gaibu ba, Kar kace masa Wallahi Tallahi ANNABI S.A.W yasan gaibu bazaku fahimci juna ba.

Abunda zakayi sai ka tambaye shi menene gaibu? 

Idan mai ilimi ne zai ce maka Allah Qaibu ne Sai ka tambaye shi
"toh Allah ne ANNABIN bai sani ba" ??

Zai sake ce maka mala'iku qaibu ne,
L sai kace masa ai

"Mala'ikun yan aiken sa ne.
Ai aiken su ya keyi S.A.W"

Ba ANNABI S.A.W ba, wanda ma ya zauna
kusa dashi sai ya gansu. 

Su Mala'ikun kuma Zai sake ce maka Aljanna da wuta Qaibu ne Sai kace masa

"Ai Ana zaune a duniya Manzon Allah ke zuwa ya dawo har yace yaga wane kaza acikin wuta kuma yaga wane kaza acikin aljannah"

"Ana zaune zai ce ga Aljanna ga wuta a gabana ku kuna ganin bango shi yana ganin Aljanna"

Zai sake ce maka abunda zai faru nan gaba Qaibu ne! Sai kace masa

"A tsayuwa daya ANNABIN ya
bada labarin abinda zai faru har tashin
Alqiyama"

"KANA FEENA RASULULLAHI S .A .W
MAQAMAN FAMA TARAKA SHA'IN TAKUUNU FI MAQAMA MIHI ZALIKA ILA QIYAMISSA'ATI ILLAH HADDASANA BIHI"

Allah yakarawa Professor lafiya da fahimta bijahi S.A.W - Ameen

Post a Comment

 
Top