WANNAN ITA CE AQIDARSA

Zamuji daga Bakin Shehu Ibrahim Inyass RA, ko akan wace Akidar yake?

A Shekarar 1961, a Makka Wani Dan Jarida Abdulkareem Niyyaziy ya tambayi Shehu kan Mazhabarsa?

Sai yace: Ni ina kan Mazhabar Malikiyya ta Liman Gidan Hijra, Malik Dan Anas RA, kuma a bisa AKIDAR Ahlus Sunnah Wal Jamaa'a, Yazo a shafi na 74, a littafin

ﻣﺎﺫﺍﻗﺎﻟﺖ ﺍﻟﺼﺤﻒ ﻭﺍﻻﺫﺍﻋﺎﺕ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؟

A cikin Diwani na 6, MANAA SIKU.. yace: Baya yarda da duk abinda ba Tauhidi ba

ﺍﺑﻴﻨﺎﺳﻮﻯ ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺘﻰ **
ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺼﻄﻔﻰ ﺗﺮﻭﻯ ﻭﺍﻥ ﺻﺤﺒﻪ ﺗﺮﻭﻯ ***
ﺍﻓﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺷﻚ ﺍﻭﺑﺄﺣﻤﺪ ﻓﺎ ﺳﻤﻌﻮﺍ **
ﻓﻜﻞ ﺳﻮﺍ ﻩ ﻣﻔﺘﺮ ﻛﺬﺏ ﺩﻋﻮﻯ ***

Munki duk abinda ba Kaidaita Allah ba, sai kuma Sunnar da aka karbo daga Annabi saw aka ruwaito daga Sahabbai RA

Yanzu akwai kokanto a samuwar Allah ko a manzancin Annabi Ku saurareni, duk abinda ya saba wannan Korarrene Karya ne!

Wani wuri yace:

ﻓﺄﺷﻬﺪ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻﺭﺏ ﻏﻴﺮﻩ **
ﻭﻗﺪ ﺑﻠﻎ ﺍﻟﻤﺨﺘﺎﺭ ﻭﺍﻧﺰﻫﺖ ﺍﻻﺳﻮﻯ ***

Ina shaida cewa, Allah ba abin bauta da Cancanta waninSa, kuma Ina shaida Annabi Zababbe, ya isarda sako yagusarda duk mugun abu
A wani Wuri yace:

ﻧﻜﺮﺭﺣﻘﺎ ﻻﺍﻟﻪ ﺳﻮﻯ ﺍﻟﺬﻯ **
ﻟﻪ ﺍﻟﺨﻠﻖ ﻭﺍﻻﻣﺮ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ﺍﻟﺘﻤﻨﻊ ***

Muna maimaitawa ba abin bautawa da Cancanta sai Allah Wanda shi kadai keyin Halitta yake baada Umurni
SHEHU YAYI IMANI DA DUK ABIDA AKAYI UMURNI DASHI

ﻧﻮﺣﺪ ﻣﻮﻻﻧﺎ ﺑﺄﺣﻤﺪ ﻧﻮﻣﻦ **
ﻭﺑﺎﻟﺮﺳﻞ ﻭﺍﻻﻣﻼﻙ ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻤﻬﻴﻤﻦ ***

Muna kadaita Allah Ubangijinmu munyi Imani da Annabi Ahmad da sauran Manzanni da Mala'iku (da duk abinda yake Wajibi Imani dashi kamar Kaddara)
Shiyasa wani wurin yace:

ﺍﺫﺍ ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻻﻗﺪﺍﺭ ﻣﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺍﻟﻤﻠﻚ **
ﻓﺴﻴﺎ ﻥ ﻋﻨﺪﻯ ﻣﺎ ﻳﺴﺮ ﻭﻣﺎ ﻳﺒﻜﻰ ***

Tunda Allah ne me hukunta kaddara, to ni a wajena duk daya ne, abinda kesa farin cikin da mai Saka kuka

SHEHU NA GARGADI AKAN SHIRKA

ﺩﻋﻮﻧﻰ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﺜﻠﻴﺚ ﻭﺍﻟﺸﺮﻙ ﻭﺍﻋﺒﺪﻭﺍ **
ﺍﻟﻬﺎ ﺑﺮﺍﻻ ﻻ ﺷﺮ ﻳﻚ ﻟﻤﻦ ﻣﻠﻚ . ***

Ku bar zancen Trinity cewa Allah uku ne, kubar Shirka, Ku bautawa Allah Mai Halitta, baya da abokin Tarayya a cikin abinda ya Mallaka

SHEHU NA KIRA AYI TAUHIDI
ﺗﻌﺎﻟﻮﺍ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻮﻯ ﻟﻨﻌﺒﺪﻥ **
ﺍﻟﻬﺎ ﺑﺮ ﺍ

Post a Comment

 
Top