TATTAUNAWA TA MUSAMMAN AKAN
MAS'ALAR MASU JINGINA KAFIRCIN YAN
JABUN HAKIKA GA TIJJANAWA.

Idan Kai Mai Karatu Ka Zamo Alkalin
Kotun, To Ni Kuma Ayi Mun Lamunin
Zamowa Lauya, Da Fatan Zaka Karanta
Cikin Nutsuwa, Domin Yanke Hukuncin Da Ya Dace Akan Wannan Mas'ala.

Zaman Kotu Kashi Na (1).

ALKALI: Muna So Bangaren Wadanda Ake
Zargi (Tijjanawa) Bisa Tarayyar Su, Da
Yan Hakika, Da Su Kare Kansu, Bisa
Hujjoji Gamsassu Akan Ababen Da Ake
Zargin Su Dashi Na Ta'asubanci, Sa6o
Da Ketare Iyakar ALLAH Cikin Wake
Waken Su.

LAUYA : Abisa Ga Girmamawa Gareka Ya
Mai Shari'a.

Lallai Akwai Rashin Adalci Cikin Abinda
Wasu Ke Jingina Mana, Na Laifin Jama'ar
Da Suke Nasabta Kawunan Su Zuwa Da Suke Nasabta Kawunan Su Zuwa Gare
Mu, Alhali Kuma Sun Sa6a Da Duk
Koyarwar Darikar Mu, Hasali Ma Sun
Kasance Masu, Kalubalanta Gami Da
Kishiyantar Dukkanin Ababen Da Ta Ginu
Akai.

ALKALI :- Kotu Na Buqatar Kayi Mata
Bayani Dalla-Dalla, Tayaya Akayi Suka
Sa6a Ma Koyarwar Darikar Ku, Alhali
Suma Suna Ikirin Yan Darikar Ne, Kuma
Suna Nasabta Kansu Zuwa Ga Babban
Shehin Darikar Taku Sheikh Ibrahim
Inyass .

LAUYA : Kamar Yadda Kowa Yasani,
Addini Shine Ke Hukunci Akan Abinda
Mabiyin Sa Ya Aikata, Sam Sam, Ba'a
Hukunta Addini Da Ta'asar Mai Ikirarin
Bin Sa.

Wadannan Mutane Sun Sabawa Ka'idoji
Da Karantarwar Darikar Tijjaniyya Ta
Fuskoki Mabambanta Kamar Haka.

* Yana Daga Cikin Sharadin Wannan
Darika, Ba'a Baiwa Kowa Sai Musulmi,
Mai Yin Sallah Cikin Jam'i, Su Kuma
Wadannan Basuyin Sallar Ma,

* Cikin Sharadin Darikar, Ba'ayarda
Mabiyanta Yasha Koda Taba (Sigari) Ba,
Su Kuma Wadannan Har Giya Suna Sha.

* Wannan Darikar Ta Ginu Akan Neman
Gafarar ALLAH Bisa Zunubai, Ta Hanyar
Lazimtar, "Isrigfari" Sau 230 A Yini, Bisa
Sharadinta, Su Kuma Wadannan Basu Ma
Yarda Abinda Sukeyi Zunubi Bane Balle
Su Nemi Gafarar ALLAH Akai.

* Yan Darikar Na Lazimtar, "Salati Ga
MANZON ALLAH (SAW)" Sau 250 Bisa
Sharadinta A Yini, Da Kuma Yawaita
Kasidun Yabon Shi, Domin Neman
Kusanci Da Shi, Su Kuma Wadannan
Suna Keta Alfarmar Sa, Suna Fadin
Maganganu Na Izgili Akan Shi.

* Yan Darikar Na Lazimtar "Hailala" Sau
300 A Kullum Domin Tsarkake Zatin
ALLAH, Da Neman Falalar Sa, Su Kuma
Sun Kasance Masu Shirka Da ALLAH,
Tare Da Fajirce Masa.

* Yan Darikar Tijjaniyya Na Karanta
Kur'ani Su Hardace Shi Harma Da
Rubutashi Gami Da Aiki Dashi, Su Kuma
Wadancan Suna Fatali Da Kur'ani Gami
Karyata Hukunce-Hukucen Cikin Sa.

Sannan Zancen Cewa Suna Nasabta
Kawunan Su Ga Babban Shehin Darikar,
Wato Sheikh Ibrahim Inyass (rta), To Tuni
Shi Shehin Ya Barranta Dasu Ya Mai
Girma Mai Shari'a.

ALKALI : Yaushe Ya Barranta Dasu Muna
Buqatar Hujja Akan Haka.

LAUYA : Tabbas Ya Barranta Dasu Cikin
Risalar Sa, Gama Kadan Daga Abinda
Yake Cewa.

ﺍﻣﺎ ﻣﻦ ﻳﻨﺘﺴﺐ ﺍﻟﻴﻨﺎ ﻭﻳﺮﺗﻜﺐ ﺷﻴﺌﺎ ﻣﻦ ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ
ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﺍﻟﻤﻄﻬﺮﺓ ﺍﻟﺸﺮﻳﻔﺔ ﺑﺎﻗﺘﺤﺎﻡ ﺍﻟﻤﺤﺮﻣﺎﺕ ﻭﺗﺮﻙ
ﺍﻟﻤﺄﻣﻮﺭﺍﺕ ﻓﺄﺷﻬﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺷﻬﺪﻛﻢ ﺍﻧﻰ ﺑﺮﻱﺀ ﻣﻨﻪ ﺍﻟﻠﻬﻢ
ﺍﻧﻰ ﺑﺮﻱﺀ ﺍﻟﻴﻚ ﻣﻤﺎ ﺻﻨﻊ ﻫﺆﻻﺀ

MAI SHARI'A : Ka Fassarawa Kotu Abinda
Shehun Ya Fadi Da Harshen Hausa. "

LAUYA : Abinda Yace Shine " Amma Duk
Wanda Ya Nasabta Ko Jingina Kansa
Zuwa Gare Mu (Da Soyayya Ko Da Wani
Aiki), Kuma Yazamo Yana Aikata Wani
Abu Da Ya Sabama Shari'a Abar
Tsarkakewa, Madaukakiya, Ya Zamo Mai
(Aikata) Ababen Da ALLAH Ya Haramta,
Tare Da Nisantar (Aikata) Ayyuka
Kyawawa Na (Musulunci), Ina Neman
Shaidar ALLAH, Kuma Kuma (Almajirai
Na) Ku Shaida, Ni Na Barranta Daga
Gare Shi, Ya ALLAH Ni (Ibrahimu) Na
Barranta, Daga Kirkire-Kiren Kowaye"

ALKALI : Hakane! To Amma, Tunda Suna
Amfani Da Sunan Darikar Ku, Da Kuma
Sunan Babban Shehin Darikar Ku, Ai
Hakan Na Nufin Duk Laifin Da Suka
Aikata Zai Shafe Ku.

LAUYA : Ya Mai Girma Mai Shari'a A
Hukunci Na Shari'ar Addinin Musulunci,
Laifin Mai Laifi Bai Shafar Wani Saboda
Nasaba, Ko Kusanci, Ko Kuma
Dangantaka, Muddin Basuyi Tarayya
Cikin Aikata Shi Ba.

Domin Yazo Cikin Littafin ALLAH Sura Ta
6 Aya Na 164 Inda ALLAH (SWT) Yake
Cewa

ﻭَﻟَﺎ ﺗَﺰِﺭُ ﻭَﺍﺯِﺭَﺓٌ ﻭِﺯْﺭَ ﺃُﺧْﺮَﻯٰ ۚ

Ma'ana " Kuma Babu Wani Mai Daukar
Nauyi, Da Zai Dauki Nauyin (Aikin Sabon)
Wani ( Duniya Da Lahira)."

Sannan Kuma ALLAH Ya Kuma Fadi Cikin
Littafin Sa Sura, 2 Aya Na 282 Yace.

ﻟَﺎ ﻳُﻜَﻠِّﻒُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻧَﻔْﺴًﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﻭُﺳْﻌَﻬَﺎ ۚ ﻟَﻬَﺎ ﻣَﺎ ﻛَﺴَﺒَﺖْ ﻭَﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ
ﻣَﺎ ﺍﻛْﺘَﺴَﺒَﺖْ

Ma'ana " Kuma Baza'a Daurawa Rai
Aikata, Abinda Bazata, Iya Ba, Ladar
Abinda Ta Aikata Mai Kyau Yana Gareta,
Kuma Zunubin Da Ta Aikata Yana Gare
Ta"

Bisa Duba Ga Wadanan Ayoyi, Ne
Yasanya, Dan Gidan ANNABI NUHU (As)
Aikin Sa Da Ya Bambamta Da Na
Mahaifin Sa, Sai Ya Hallaka.

Munafukan Da Suka Tare A Fadar
MANZON ALLAH (SAW) Zaman Su Dashi
Bai Amfane Su Ba, Kasancewar Su Sun
Kafirce Masa.

Saboda Haka, Ya Mai Girma Mai Shari'a,
Sam-Sam Laifin Mai Laifi, Bai Shafar
Al'ummar Da Ya Jingina Kansa Zuwa
Gare Su, Muddin Basuyi Musharaka Cikin
Aikata Zunubi Ba A Shari'ance.

Post a Comment

 
Top