YADDA AKEYIN LAZIMIN SAFE DA NA YAMMA DA WAZIFA DA KUMA ZIKIRIN JUMA'A.

1. LAZIMIN SAFE DA NA YAMMA DA YADDA AKE YIN SU.

Lazimi shine Karanta abubuwa guda uku:-

1. Istigfari=100, 2. Salatul FATIHI=100, 3. Hailala=100.

Muridin DARIQAR Tijjaniyya zai Karanta kamar yadda yake a haka bayan Sallar Asuba da sannan kuma da bayan Sallar la'asar wato da yamma kenan, kuma a jere yadda suke haka. Bayan mutum yayi niyya, Ta'awuzi da Basmala, FATIHA 1,

Sai kuma fadin "Subhana Rabbika Rabbil-Izzati Amma Yasifun Wa-Salamun Alal-Mursalin-Wal-Hamdu Lillahi Rabbil-alamin", sau daya bayan Istigfari 100, da Salatul FATIHI 100.

Sannan kuma bayan Hailala 100, Sai ace:

"Sayyidina Muhammadu Rasulillahi Alaihi Salamullahah" Sau 1.

Sannan kuma sai ayi

"Subhana Rabbika Rabbil Izzati Amma Yasifun Wa Salamun Alal Mursalin Walhamdulillahi Rabbil Alamin" sai 1.

Sai kuma akaranta addu'ar rufewa wato "Allahumma Antal Auwalu.........

Addu'ar Sheikh Ibrahim Niasse R.A.

Bambancin lazimin safe da na yamma niyya ce kawai, Kamar yadda insha Allahu bayani zai zo a Nan gaba.

Babu laifi ga muridi ya Karanta dogon Istigfari kamar wanda mukeyi a Wazifa, ko Kuma gajere kamar "Astagfirullah, a yayin Istigfari 100.

Babu laifi ga muridi ya Karanta kowanne siga/nau'i na salati a laziminsa, Sai Dai kamar yadda Sheikh Ibrahim Niasse R.A.

Ya fada a cikin RUHUL adab cewa: "mu lizimci Karanta salatul FATIHI sabida falalarta.

2. WAZIFA SAU DAYA AKEYI A KULLUM.

ABUBUWA GUDA HUDU AKE KARANTAWA A WAZIFA SUNE KAMAR HAKA:-

1. Astagfirullah Azimal Lazi La'ilaha Illahuwal Hayyul Qayyum=30.

2. Salatul FATIHI 50, 3. Hailala 100, 4. Sai kuma Jauharatul Kamal Kafa 12, ko Kuma Salatul FATIHI Kafa 20 a maimakon Jauharatul Kamal.

Ana kuma fadin "Subhana Rabbika".............

Sau 1 bayan Karanta Salatul fatihi.

An kuma fadin "Sayyidina Muhammadu Rasulillahi Alaihi Salamul-Lahi" Sau 1 bayan Hailala ta karshe.

Sai kuma fadin "Innal Lala Wa Mala'ikatahu Yusalluna Alan Nabiyyi, Ya Ayyuhal Lazina Aamanu Salluu Alaihi Wa Sallimuu Tasliman........

Subhaana Rabbika Rabbil Izzati Amma Yasifun Wa Salamun Alal Mursaliin Walhamdu Lillahi Rabbil Aalamin. Sau daya bayan Jauharatul Kamal.

Sannan Mukaddami ya Karanta "Allahumma Antal Auwalu" Sau daya, da sauran addu'o'in da Suka samu da Azkarai na Dafa'i da kuma Jalabi kamar yadda aka saba".

Lallai ne muridi ba zai Karanta wani siga na salati ba a cikin wazifa sai Salatul Fatihi.

Ana budewa da Niyya, Ta'awuzi, Basmala, Karanta FATIHA har zuwa karshe Sau daya.

3. ZIKIRIN JUMA'A SAU DAYA A SATI.

Shine ZIKIRIN da ake taruwa a masallaci da yamma a Ranar juma'a daga misalin awa daya kafin faduwar rana, Har izuwa fadawar rana.

Ayi tayin "LAA'ILAAHA ILLALLAH" babu adadi, ko Kuma Allah Allah ko Kuma dukka biyun, Har izuwa faduwar rana.
!
!
Ana budewa da Niyya, Ta'awuzi, BASMALAH, FATIHA 1, Sai "Istigfarin Wazifa Sau 3, Sai Salatul Fatihi 3 sai

"Subhana Rabbika....... Sau 1 ashiga Zikiri.

Hakanan ana rufewa da abinda aka Bude da shi. Sai ayi addu'o'i, Bayan Mukaddami ya Karanta "Allahumma Antal Auwalu" kamar yadda ake yi bayan Wazifa. Allah S.W.T. Shine Masani.

Post a Comment

 
Top