HANYAR ZUWA WURIN ALLAH....

Idan mai bautar Allah ya fara zikiri, to shi da ma aikin zikiri shi ne tsaftace zuciya, ya mayar da ita kaman madubi, idan ta zamo haka tamkar madubi sai hoton hasken Ubangiji ya bayyana a cikin ta,..

Bayyanar hoton hasken Ubangiji yakan haifar da wani jin dadi na ban mamaki, babu wani harshe a duniya da zai iya sifanta wannan jin dadin, ko ya yi bayani akan sa, ko ya sifanta yanda yake, babu wanda zai sani sai wanda shi ma ya sami kansa a cikin irin wannan jin dadin, duk wanda ya dandana kam zai san me ake ciki, ba kuma za a iya sani ba sai da gwaji..

Zikiri kam shi ne matakala ta farko a wannan hanyar, shi ne zai kai zuwa ga tsarkake zuciya, ta yanda za ta zamo tamkar madubi, shi kuwa mai waige - waige kam, babu inda zai kai..

Idan na ambaci Allah, sai na sami kai na a cikin wani hali, na kuma shagaltu da wannan halin, to na fara waige - waige kenan, daga nan ne kuma mafarin rudu da halaka, na shiga cikin abubuwa masu dauke hankali kenan, da haka sai ya zamo ba domin Allah shi kadai na kama hanya zuwa gare shi ba..

A dalilin haka ne suka ce dole ne a sami Shaihi ga duk wanda yake son bin wannan hanyar, Shaihin da zai rika fadakar da muridi, domin ya sake dawowa kan tsakiyar hanya.

Kuma dole shi Shaihin ya zama ya riga ya bi wannan hanyar karkashin karantarwar da ba ta saba da littafin Allah da Sunnar Manzon Allah ba, bal ma take da dalilai masu karfafa ta daga cikin littafin Allah da sunnar Manzon Allah, kaman dai yanda halin Annabi MUHAMMADU (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake tare da Sahabbai, ko halin Sahabbai tare da masu biye masu cikin Tabi'ai, har zuwa wannan lokaci da muke ciki...

Shi kansa Shaihin nau'i - nau'i ne, kuma mataki - mataki ne, sai dai dole ne duka su kasance sun san hanyar a farko, sun kuma san nau'o'i iri - iri na abubuwan da suke dauke hankali da suke kewaye da hanyar, sun kuma san yanda za su yi nasiha, sun kuma san yanda za su koyar da yanda ake yi wa Allah ladabi; domin yi wa Allah ladabi babban ginshiki ne a cikin wannan hanyar...

Farkon abin da Shaihi zai karantar da muridi shi ne : yanda zai yi zikirin Allah, na biyu kuma : ya koya masa rashin waige - waige, in ba fuskantar Manufa ba...

#Hanyar_zuwa_wurin_ALLAH

Sheikh Aliyu Juma'a Muhammad

Tarjama : Saleh Kaura

Post a Comment

 
Top