RAYUWA CIKIN TIJJANIYYA RAYUWA CE MAI TSABTA..

Idan Ka Siffata Ko Ka Kwatanta Darikar Tijjaniyya Da Sauran Firkoki Ko Kuma Kungoyiyin Addinin Musulunci, Anan Ne Zaka Gane Lallai Zamowa Batijjane Wani Alkairi Ne Babba Daga ALLAH, Ga Wasu Zababbu Daga Bayin Sa, Bisa Duba Ga Irin Tsabtar Da TijjaniyarKe Tattare Dashi...

KUMA MUDDIN BATIJJANE YA TAFIYAR DA RAYUWA BISA HAKIKANIN KOYARWAR SHEHU TIJJANI,
TO DA YARDAR ALLAH ZAI KASANCE CIKIN WADANDA ZASU AMSHI TAKARDUN AYYUKAN SU DA HANNUN DAMA...

Tijjiyya Tana Shiryar Da Ma'abocin ta Kulawa DaHakkin Abubuwa Kamar Hakka...

RIKO DA IBADU DA KIYAYE IYAKOKIN ALLAH...

TIJJANAWA, MA'ABOTA KIYAYE IYAKAR ALLAH NE (Basu Ketara Dokokin Sa Da Gangan) SANNAN MASU KULAWA DA BAUTAR SANE,, KAMAR YADDA ALLAH YAKE SIFFATA BAYIN SAMANAGARTA DA WADANNAN SIFFOFI A QUR'ANI SURA TA 9 AYA NA 112...

ﺍﻟﺘَّﺎﺋِﺒَﻥﻮُ ﺍﻟْﻌَﺎﺑِﺪُﻭﻥَ ﺍﻟْﺤَﺎﻣِﺪُﻭﻥَ ﺍﻟﺴَّﺎﺋِﺤُﻮﻥَ ﺍﻟﺮَّﺍﻛِﻌُﻮﻥَ ﺍﻟﺴَّﺎﺟِﺪُﻭﻥَ ﺍﻟْﺂﻣِﺮُﻭﻥَ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﺍﻟﻨَّﺎﻫُﻮﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨْﻜَﺮِ ﻭَﺍﻟْﺤَﺎﻓِﻈُﻮﻥَﻟِﺤُﺪُﻭﺩِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ۗ ﻭَﺑَﺸِّﺮِ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ .

.Ma'ana "Masu Tuba Ne (A Kullum), Masu Bautane ( Ga ALLAH Saboda Chanchantar Sa) Masu Godiyane ( Ga Ni'imomin ALLAH) Masu Tafiya Ne ( Domin Sadar Da Alkairi) Masu Ruku'u Ne (Domin Girmama Mahaliccin Su); Kuma Masu Tawali'u Ne (Basu Da Girman Kai), Sannan Masu Umarni Da (Aikata) Alkairi, Kuma Masu Hani Da Aikata Sharri; (Akwai Malamai Acikin Su) Masu Kiyayewa Ne Ga Iyakokin ALLAH (Basu Ketarewa Wajen Shan Giya Zina Dsrnsu), Kuma (YARASULULLAH) Ka Bayar Da Bushara Ga Muminai"..

Wannan Aya Ta Tattare Dukkanin Kyawawan Suffofi Na Ainihin Batijjanen Kwarai, Saboda Haka Kasancewa Cikin Rayuwa Mai Dauke Da Irin Wadannan Siffofi Alkairi Ne Babba....*

GIRMAMA HAKKIN SHUGABA (SAW)..

Idan Akayi Duba Izuwa Ga Asusun Batijjane Ga Wannan; Shi Kadai Ya Isheshi Garabasa Mafi Girma, Domin Litattafan Wannan Darika, Da Malamanta, Kullum Burin Su Shine, Duk Wata Kalma Ko Harafi Da Zasu Firta Akan SHUGABA (SAW) To Suna Furta Kalmar Girmamashi Ne Da Girmama Kususiyar Sa, Sam Basu Tauye ANNABI (SAW) Da Kwayar Zarrar Harafi Na Rubutu Ko Na Magana..

Tijjaniya Ta Koyar Da Duk Wani Ma'abocin Ta, Rayuwa Cikin Tsananta Soyayya Ga MANZON ALLAH (SAW) Domin Sai Da Sonsa Samada SonKomai Tukunnah Imani Ya Cika..Lallai Rayuwa Cikin Tijjaniyya Rayuwace Mai Tsabta

Domin ANNABI (SAW) Yace
" ﺍﻟْﻤَﺮْﺀُ ﻣَﻊَ ﻣَﻦْ ﺃَﺣَﺐ

.".Ma'ana" Masoyi, Yana Tare Da Masoyin Sa"...*

GIRMAMA HAKKIN IYALAN GIDAN MANZON ALLAH (SAW)..

IDAN AKAYI DUBA IZUWA GA HAKKIN IYALAN GIDAN MANZON ALLAH (SAW)
TIJJANAWA SUNA GIRMAMA DUKKANIN SU, SUNA MARTABA SHA'ANIN SU, BASU ZAGI KO KYARAR KOWANNEN SU, KAMAR YADDA WASU MARASA RABO SUKEYI...ANNABI (SAW) KUMA Yace.

ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺪﺧﻞ ﻗﻠﺐ ﺍﻣﺮﺉ ﻣﺴﻠﻢ ﺇﻳﻤﺎﻥ ، ﺣﺘﻰ ﻳﺤﺒﻜﻢ ﻟﻠﻪﻭﻟﻘﺮﺍﺑﺘﻲ

‘.Ma'ana "Wallahi, Imani Bazai Shiga Zuciyar Wani Musulmi Ba, Har Sai Ya Kaunace Ku (Ahlil Baiti) Saboda ALLAH Da Kuma Dangantaka Ta Daku (Ahlil Baiti) (Aduba Musnad Na Imam Ahmad Mujallabi Na 1 Shafi Na 342 Kan LambarHadisi Na 1780.)..

Madallah Da Wannan Rayuwa Mai Tsabta Da Cikinta Babu Zagin Jikokin MANZON ALLAH (SAW)...*

BANGAREN MARTABA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW).

Tijjanawa, Sun Tafi Akan Fahimtar " Wal'imsaku Amma Shajara Bainahum" Wato Kame Baki Akan Duk Abinda Ya Faru Tsakanin Su, Tare Da Nemar Musu Gafara Baki Daya Da Nemar Musu Mafi Kyaun Matafiya A Lahira Domin Sune Mafiya Chanchanta Da Yiwa Hakan..

TIJJANAWA SUNBI WASIYYAR MANZON ALLAH (SAW) WAJEN KIYAYE HARASAN SU DAGA ZAGIN SAHABBAN SA...

MANZON ALLAH (SAW) Yace " Kuji Tsoron ALLAH Cikin Duk Wani Sha'ani Da Ya Shafi Sahabbaina, Kada Ku Mayar Dasu Ababen Musgunawa Abayana, Duk Wanda Ya Kaunace Su, To Ya So Su Ne Saboda Sona, Duk Wanda Ya Kisu, To Ya Kisu Ne Domin Kina, Duk Wanda Ya Fitine Su, To Ni Ya Fitina, Sannan Duk WandaYa Fitinen To ALLAH Ya Fitina, Kuma Duk Wanda Ya Fitini ALLAH To Lallai Tababbe Ne DaALLAH Zai Masa Mummunan Kamu (ranar lahira).

Aduba Miskat Al Masabi, A Littafin Tirmizhi Kan Lambar Hadisi Na 5534...

MANZON ALLAH (SAW) Yace,
" Tsinuwar ALLAH, Da Ta Mala'ikun Sa, Da Ta Mutane Baki Daya Ga Duk Wani Wanda Ya Zagar Mun Sahabbaina. (Ibn Hajar Al Haisami, A Majma'a AlZawa'id).

A Wani Hadisin Kuma Yace" Kada Ku Zagar MunSahabbai Na, Ina Rantsuwa Da Mamallakin Rai Na, Da Ace Dayan Ku Zai Batar Da Zinare Kwatankwacin Girman Dusten Uhudu, A Hanyar ALLAH, Ladar Sa Bazai Kai Ladan Zinare Cikin Hannu Daya Ko Rabin Sa Da Sahabina Ya Batar Ba..

(bukhari Da Muslim)..

SABODA HAKA, BATIJJANE A HAKKIN SAHABBAI, DUK CIKIN SU GUDA 114,000 BABU DAYA ABIN ZAGI, KO AIBATAWA A WAJEN SA, BALLE CI MUSU MUTUMCI TA KOWANNE JANABI..Gayamun Rayuwa Mafi Tsabta Irin Ta Batijjane.?..*

MARTABAR WALIYYAN ALLAH (SWT)..Cikin Waliyyan ALLAH Baki Daya, Babu Wani Da Tijjanawa Ke Zagi Ko Suke Munanta Zance AkanSa, Kamar Yadda ALLAH Yayi Hani Da Hakan....

LALLAI TIJJANIYYA ITACE HANYAR RAYUWA MAFI TSABTA CIKIN ZAMANINA.

Post a Comment

 
Top