Hanyoyin amfani da ruwan lemun tsami ya ke inganta kiwon lafiyar dan Adam Ga masu neman hanya mafi sauki don inganta rayuwar su da kuma lafiyar su fiye da komai, shan ruwan lemun tsami a farkon kowace safiya abu ne mai sauki da mutum zai rinka yi kuma zai yi tasiri wajen lafiya managarciya.

 Da yawan mutane da suka dauki wannan al'ada shekaru kadan da su ka gabata, sun bayyana irin tasirin da suka samu wajen inganta lafiyar su da lemun tsami ke yi.

 Bisa ga falsafar Ayurvedic, zabin kiwon lafiya da kake yi game da aiki na yau da kullum ko dai ya karfafa juriya ga cututtuka ne ko kuma ya yada ta. 

Lemun tsami yana kunshe da sunadaran vitamin C, B, calcium, iron, magnesium, potassium, enzymes, antioxidants, da fibers. Ga fa'idojin shan ruwan lemun tsami a jikin dan Adam kamar haka: 

Inganta narkewar abinci cikin gaggawa Tsarin ruwan lemun tsami yana kamanceceniya da ruwan cikin mutum saboda haka yana taimakawa wajen narkar da duk wani nau'in dafi ko guba ta abinci. 

Ruwan lemun tsami yana taimakawa wajen narkewar abinci cikin sauki, kwarnafi da tashin zuciya, sannan yana sanya bayan gida mai laushi ba tare da wahala ba.

 Ruwan lemun tsami ya na da sunadarin vitamin c, wanda ya ke karfafa garkuwa mai yakar cututtuka ta jikin dan Adam, sannan kuma akwai sunadarin iron wanda ya ke taimakawa wajen tato duk wani sunadarin iron na cikin abinci.

 Samar da wadataccen ruwa a jiki. Jikin mutum yana da matukar bukatar ruwa a kowane lokaci, saboda haka jikin mutum ya zama cikin yalwar ruwa abu ne mai fa'ida kwarai dagaske.

 Shan ruwan lemun tsami a kowace safiya zai taimakawa jikin dan Adam zama cikin wadataccen ruwa domin kuwa sai da ruwa kowane sashe na jikin zai yi aikin da ake bukata. 

Shan ruwan lemun tsami yana sanya karfi a jikin dan Adam tun daga lokacin da aka sha shi. 

Gyaran fata Lemun tsami yana da sunadaran antioxidants da suke bayar da kariyar wajen yamushewar fata.

 Wanna sunadaran su na taimakawa wajen hana tsufan fata ta tamushewa, ta yadda hausa kan ce'mayar da tsohuwa yarinya'. 

Shafa ruwan lemun tsami a kan fuska ba tare da shiga cikin rana ba, ya kan taimaka wajen kauda kurajen fuska, kyasfi, makero, amosani da sauransu. 

Yana sa fuska ko kuma fata ta kara kyau matuka. 

Ruwan lemun tsami su na da ikon cire sunadaran uric acid daga gabbai saboda shi uric acid shine mai assasa kumburi a jikin dan Adam. 

Taimako wajen rage nauyin jiki Lemun tsami shi kadai baya rage nauyin jiki, amma yana taimakawa wajen hana saurin jin yunwa domin yawan cin abinci yana assasa jikin mutum ya yi nauyi.

 Ana amfani da burushin wanke baki da ruwan lemun tsami a wanke hakora domin su fita kar. 

Haka kuma baki zai bar wari, amma kar a rinka wankewa akai-akai sai lokaci bayan lokaci saboda zai iya raunana karfin hakora.

 Amfani da ruwan lemun tsami yana kawar da warin kashi ko kuma hammata. 

Idan aka shafa lemun tsami a hammata zai kauda wannan wari. 

Sabon raunin da bai wuce hankali ba, da zarar an matsa mai lemun tsami zai kame ya warke. 

Haka kuma shan ruwan lemun tsami da Lipton yana rage karfin sha'awa Sai dai wani hanzari ba gudu ba, idan mace ta yawaita amfani da Lemon tsami to zai rage mata sha'awa. 

Haka mata masu ciki kada su yawaita amfani da Lemun tsami. 

Masu gyambon ciki wato Ulcer, su ma su kula wajen shan lemun tsami. 

Amma dukkanin wadannan zai musu illa ne in sun sha a ciki ba wai shafawa ba.

 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top