Jarumar ta bayyana mana Hakan ne a wata Zantawa da suka yi da wakilin mu dangane da shigowar ta masan Fina Finan Hausa ta kannywood da kuma yadda tauraruwar ta take haskawa a cikin kankanin lokaci.
Jarumar ta fara da cewa " Abin da zan iya fada shi ne, daukaka ta zo mun ne ba zato ba tsammani. Na yi tunanin zan sha wahala sosai , Amma cikin Ikon Allah da na zo sai naga akasin haka ban sha wahalar da nake tunani ba. Wanda A lokaci kadan Allah ya daukaka ni har ta kai ga idan na fita ana gane fuska ta har a ce ga Amal! Idan na je wuri a ce ga Amal , to babu abin da zan ce sai godiya ga Allah.'
Da muka tambaye Jarumar wani fim ne take ganin ya fito da ita har duniya ta fara sanin ta? Sai ta amsa da cewa ce " wani fim ne mai suna"Rabu Da Maza," kuma har yanzu fim din bai ma fita kasuwa ba , amma saboda yadda wakokin shirin suka yi ta yawo a duniya , hakan ya sa ya fito mun da martaba ta, Sanan na biyun sa kuma shi ne "Larai Ko Jummai," don ko wani waje na je sai ka ji ana cewa, Laa ! ga Jummai , ni da kawata Maryam Yahaya muka fito a fim din.
Jarumar ba fim din Hausa kadai take yi ba ta kan fito har a cikin finafinan kudu, don haka muka tambaye ta ko me ya ja hankalin ta har ta shiga finafinan kudu?
Sai ta amasa da cewa: Toni dai gaskiya ban taba tunanin zan tafi kudu ba, ban kuma taba sanyawa a rai na zan je kudu in yi fim ba.
Taci gaba da cewa; Wata rana ina zaune, sai maigidana Yakubu Muhammad ya kira ni a waya ya ce 'yan kudu suna so su yi aiki dani, wannan maganar tasana shiga tunani cike da mamaki , Na Amsa Masa da cewa Eh zanyi Daga nan aka hada ni da su na tura musu hotuna na da kuma wata hira da aka taba yi da ni cikin harshen turanci. Bayan na tura musu suka ga na kware da turanci zan iya yin abin da suke so shi ne suka dauke ni." Inji Amal Umar
Mun tambaye ta bata tunanin shigar ta finafinan kudu zai kawo kalubale a matsayin ta na ya Mace kuma yar arewa?
Ta amsa da cewa;"Eh toh gaskiya ni dai abin da zan iya cewa shine ko a fim din Hausa ana zagin mu, ana cewa mu 'yan iska ne wanda kuma mutane suna manta cewa tarbiyya daga gida ake samun ta, idan mutam ya samu tarbiyya tun daga gida to zai kasance mai tarbiyya a duk inda ya samu kanshi.
Wakilin mu ya tambayeta “ gaki yarinya mai kanunun shekaru, ko kina da niyar yin aure nan kusa? Da yake ita karamar yarinya ce ana yi mata ganin a yanzu kawai neman suna ne da daukaka a gare ta ba maganar aure ba.
Sai ta ce " Idan lokacin aure ya yi zan yi don ni ko yau ko gobe aure ya zo mini zan yi saboda ni ban dauki wani buri a rayuwa ta ba , don babu abin da ban samu ba dai dai gwargwadon bukata. Ina da mota, ina da shagon yin kwalliya , ina da kudi daidai gwargwado don haka babu abin da zan ce sai godiya ga Allah, ina fatan ya kara mana rufin asiri duniya da lahira."
©HausaLoaded
Post a Comment