Daga Bashir Abdullahi El-bash
"Allah ya sani, da Allah zai tambayen mai ya sa ka ce musu su zaɓi Ganduje? Wallahi akwai dalilan da na dogara da su, kuma ina sa ran Allah ya yarda da su".
"Kwanaki ya gayyace mu musuluntar da Maguzawa, Bamaguje ɗari biyu da kiristoci biyu, sun musulunta a sanadiyyar shi. Bayan wannan na samu labarin an sake yi a wudil, Bamaguje ɗari biyu ya sake musulunta".
"Ranar da mu ka je aka musuluntar da Bamaguje ɗari biyu, Allah ya sani kuka na rinka yi na ga abin da ban taɓa gani ba. In ga wahalar da mu ke sha in mun shiga ƙasashen arna kafin mu samu mutum goma, ashirin, talatin, yau ga mutum ɗari biyu da biyu a gabana za su karɓi kalmar Shahada".
"Shugaban ƙungiya na ƙasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau, sai da ya ba da kalmar shahada wa mutum talatin. Ni da kaina sai da na ba da kalmar shahada wa mutum ashirin. Gwamna sai da ya ba da kalmar shahada wa mutum talatin zuwa hamsin. Malam Ibrahim Shekakarau sai da ya ba da kalmar shahada wa mutum talatin. Haka maluma su ka rinka ba da kalmar shahada".
"Bayan an kammala wannan, dukkan waɗanda su ka musuluntan nan, kowacce mace sai da aka ba ta turmin zani aka ba ta jari da za ta yi sana'a. Idan namiji ne sai da aka ba shi turmin shadda aka ba shi jari da zai yi sana'a. Ina so duk Nageriya ku faɗa min gwamnan da ya na kan kujerar gwamna zai zauna ya na musuluntar da jama'a su na karɓar kalmar shahada ?".
"Ban ce maka bai da laifi ba, ya na da laifuffuka daiwa a wajen Allah, amma ni a wajena duk laifin da ya aikata wannan aikin alherin ya kai ya shafe laifin".
"Manzon Allah (S.A.W) ya ce ba mutum ɗari biyu ba, mutum ƙwara ɗaya tallintal ya musulunta a sanadiyyarka, ya fi muhimmanci a kan a tara jajayen raƙuman ƙasar saudiyya a ba ka. Mutum ɗaya ya musulunta a nan Kano a sanadiyyarka, wannan musulunci da ka ba shi, ya fi duk motoci jifa-jifai da ke cikin garin Kano".
"Kun san abin da zai ba ku mamaki ?, a ranar su ka ba da lissafin waɗanda su ka musulunta albarkar hanyar wannan bawan Allah (Gwamna Ganduje), wannan adadin a wannan rana mutum dubu goma sha tara da ɗari biyu da biyu. Gwamna me da'awa".
"Ba maganar su wa ake cirewa yanar ido ake ba. Masabaƙa da ake ta karatun alƙur'ani mai girma bayan wacce ake a ƙarƙashin ɗan Fodiyo, akwai musabaƙar da ake yi a nan Jiha ƙarƙashin gwamna (Ganduje), wadda a aljihunsa zai ɗauki nauyinta ba a kuɗin gwamnati ba".
"Wannan ta ƙarshe da aka yi, ina cikin shugabanni masu jawabi a taron da aka yi, na ga abin da ya ban mamaki, mahaddatan Ƙur'ani maza da mata yara ƙanana aka yi musu kyaututtuka na alfarma da girmamawa domin a yi Inkwarejin ɗin su su ƙara haddar al'ƙur'ani mai girma. Faɗa min gwamnan da ya ke yin wannan a Nageriya ?" (Sai Gwamna Ganduje).
"Yanzu Alaramma ya ke faɗa amin bayin Allah da aka taimaka Fisabilillah ciwon makantaka sama da mutum dubu ɗari da tamanin ba sa gani aka buɗe musu ido. Masallatai da aka gina wa ya san iyakar su, makarantu wa ya san iyakar su ? Wanda zai yi wannan aikin (Gwamna Ganduje), mu na yi masa kykkyawan zato. Mai laifi mai laifi ne, mai kura-kurai mai kura-kurai ne, faɗa min gwamnan da bai kuskure a Nageriya, faɗa min gwamnan da bai laifi a Nageriya ?".
Shaikh Kabir Haruna Gombe, ya yi waɗannan kalamai ne a kan mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje gabanin babban zaɓen shekarar (2019), kwanaki kaɗan bayan sun amsa gayyatar mai girma gwamna wajen Musuluntar da Maguzawa sama da mutum ɗari biyu a wannan lokaci kaɗai.
©HausaLoaded
Post a Comment