Shafin Northflix ya Wallafa
Ina kira ga Mawakan Masana'antar Fim da kuma masu Yabon Manzon Allah S.A.W da su tashi tsaye wajen neman ilimin waka kafin su fara yi.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin tsohuwar mawakiya wadda ta ga jiya kuma har yanzu ake damawa da ita Maryam Saleh Fantimoti.

Mawakiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin mu dangane da yanayin wakkokin da ake yi yanzu na Fim da kuma na yabon Manzon Allah S.A.W wanda duka ta yi fice a kowanne bangaren.

Maganar gaskiya a lokacin baya an fi yin waka a kan abin da ya danganci Fim, Ana yin waka daidai yadda sakon labarin fim din yake, shine zakaga fim yana ma`ana. Amma in kuka lura yanzu ba haka abin yakeba, Inji Mawakiyar.

Tacigaba da cewa: Don ba zan manta ba akwai wakar da na yi ta Fim, Lokacin da Jarumar Fim din ta zo za ta hau wakar sai da ta yi kuka na gaske a Fim din saboda tausayin da yake cikin wakar. Toh amma yanzu waka ta juya sai Soyayya kawai, Mu kuma a da ba haka muke yi ba.

Mun tambaye ta a kan rashin tasirin waka a yanzu, ko meye dalilin dayasa bata  daukar dogon lokaci ana yayin ta kamar a lokacin baya?

sai ta ce: to ka San ita waka tana da matakai, domin idan Allah ya Hore maka waka to matakin farko shi ne Murya, Sai Basira, idan kana da murya ba ka da basira za ka yi waka kuma za ka ci abinci, Amma, idan ka hada biyun sai ka fi cin nasara a cikin wakar." Inji Mawakiyar.

Ta Kara da cewa ita ta samu horo ne daga wajen Fitaccen Mawaki Kuma Jarumi  Yakubu Muhammad da Muddansiru Kasim su kuma duk lokacin da za su shirya waka ba sa yin waka sai mai ma'ana wannan ya sa wakokin da ake yi a baya suka fi daukar lokaci mai tsawo ana sauraron su, Wanda har manyan mutane suna sauraron su ba kamar wakokin mu na yanzu ba.

Fantimoti ta hada bangare biyu wajen yin wakoki tana wakar Fim da kuma yabon Manzon Allah (S.A.W)." Mun kuma yi mata tambaya a kan yawan korafin da ake yi na mawaka masu yabon Manzon Allah Musamman wajen furta lafazin da yake kawo Rudani. Sai ta ce; Idan Allah ya yi maka baiwar rera kawa to dole sai ka je ga wadanda suka San Minene Yabo Suka Kuma kware akai ka yi ladabi.

Amma idan ka ce za ka yi don kana da murya to akwai matsala, Ka'ida shi ne ka je wajen malamai su sanar da kai ilimin waka, kamar yanzu idan kaji wakar da na yi ta " MUKARRIMA' ai ka San ta fi karfin kai na don haka Malami na shi ne ya ba ni wannan kasidar.

Haka kuma duk wanda zai yi waka musamman abin da ya shafi  Yabon fiyayyen hallitta toh ya nemi masu ilimin abin ya yi musu ladabi su karantar da shi ba wai kawai don yana da murya ya zo ya ce zai yi  waka ko yabo ba, Maimakon yayi yabon sai ya zo ya rinka yin barna a cikin jama'a".

Daga karshe ta yi kira ga mawaka da su hada kan su, kuma su San me za su fada a cikin wakokin su.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top