Ma'aikatar sadarwa ta tarayya ta ce an ja hankalinta a kan wani sako da kamfanin sadarwa na MTN ke tura wa kwastomominsa a kan cewa zai fara cire naira hudu (N4:00) daga asusun duk wanda ya sayi katin waya na kamfanin daga asusunsa na banki.

Jama'a sun wayi gari da samun sako a wayoyinsu na hannu a kan wannan sabon tsari da kamfanin sadarwa na MTN ke shirin fara aiki da shi daga ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2019.

Ofishin minstan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, ne ya ankarar da ma'aikatar sadarwa a kan wannan sabon tsari da MTN ke shirin kaddamar wa bayan jama'a sun mika kukansu gare shi a dandalin sada zumunta na Tuwita a ranar Lahadi.

Pantami ya ce bashi da masaniya a kan sabon tsarin da kamfanin sadarwa na MTN ya bullo da shi, a saboda haka ne ya umarci hukumar kula da kamfanonin sadarwa da ke Najeriya (NCC) da ta tabbatar cewa MTN ta dakatar da wannan sabon tsari da ta bullo da shi kuma take shirin kaddamar wa a ranar Litinin.



Da yake jinjina wa Pantami a kan daukan mataki a kan lokaci, Joe Abba, tsohon hadimi a gwamnatin Buhari, ya ce yanzu haka kamfanin sadarwa na MTN ya dakatar da sabon tsarin sakamakon umarnin da Pantami ya bayar.

Jama'a na yawan korafi a kan yadda kamfanonin sadar wa a Najeriya ke bullo da tsare-tsare masu suna daban-daban domin raba su da 'yan sulallansu na yin kira a waya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top