Bana madigo Sharri Akayi Min – Jaruma Bilkisu Salisu

Wata sabuwa: Bana madigo so suke kawai su bata mini suna – Jaruma Bilkisu Salisu.

Kamar dai yadda kowa ya sani mutane sun yi kaurin suna wajen yiwa jarumai sharri akan abinda basu ji ba kuma basu gani ba, musamman ma yanzu da aka waye da amfani da kafafen sadarwa na zamani irin su Facebook, Twitter, Instagram da dai sauransu.

A wannan karon ma wata sabuwar jarumar fim ce ta masana’antar Kannywood mai suna Bilkisu Salisu, ta fito a cikin wani sabon bidiyo da ta fitar take kare kanta akan jita-jitar da ake yadawa a kanta na cewa tana yin madigo.

Ga abinda sabuwar jarumar take cewa a cikin bidiyon:

“Assalamu Alaikum jama’a sunana Bilkisu Salisu kamar yadda kuka sani, jan hankali ne nake so na yiwa masoyana da ‘yan uwana, akwai wata lamba da wata take amfani da shi wacce idan mutum yayi amfani da manhajar True Caller yana fito da sunan Nafisa Abdullahi, ban santa ba kuma bani da alaka da ita, amma tana amfani da sunana tana yiwa mutane magana ta WhatsApp tana cewa ai ni ce tana son su, tana dai maganganu marasa dadi a kaina, ma’ana tana nuna alamun tana son ‘yan uwanta mata.

“Jama’a ni ba ‘yar madigo ba ce, bana neman mata, bani da wata alaka ta kusa ko kuma ta nesa da mace idan ba mutunci ba, abinda yasa ma na fito nayi magana shine bana so maganar tayi nisa taje wani waje a dinga ganin kamar nice nake yin irin wannan harkar.

“Idan ma wani abu na yiwa wani dan Allah yayi hakuri, bani da wata matsala da kowa, mutunci ne tsakani na da kowa, duk wani wanda muka samu sabani dashi to shine ya jawo, ni bani da matsala da kowa.

“Ko wacece dan girman Allah ta daina yi mini wannan abin da take yi, idan ba haka ba kuma zamu dauki mataki a kai.”

ku duba asalin wannan posting din daga babban shafin mu Bana madigo Sharri Akayi Min – Jaruma Bilkisu Salisu mun dauko wannan posting din daga babban shafin mu wato ArewaFresh.com. ArewaFresh.com - No1√ Best Entertainment Site In Nigeria.


©Arewafresh

Post a Comment

 
Top