Inda yake bayyana masu cewa ba haka bane amma ana barin masana'antar Kannywood a baya, Saboda basa saurin farga akan cigaban da ake samu wajen kasuwancin finafinai. Wannan cigaba ne da aka samu a duniya yanzu an daina buga finafinai a faifan CD an koma yanar gizo wajen sayarwa da tallata finafinai kamar su YouTube da sauransu.
“Wannan dalilin ya sa akayi mana nisa saboda mun taru mun ta'allaqa akan wannan turbar. Yanzu haka akwai akalla fina finai sama da dari biyar a kasa wanda an yi su ba,a sake su ba saboda rashin kasuwa, saboda ko sun fito din ma adadin da za'a sayar idan an buga sai kaga ko uwar kudi ba ta fito ba sai faduwa.
Kasuwanci ne shi ne jigo na duk wata sana’a da za a yi, kuma ai mutun bazai fito da kudi ya sa a sana'ar da ba riba ba." Inji Yakubu Muhammad
Jarumin yabkara da cewa “Amma yanzu ana ta kokarin aga an fito da wasu hanyoyi kamar su NORTHFLIX wanda Jamilu Abdussalam ya bude idan mutun ya biya kudi zai kalli fim a cikin sauki, akwai YouTube channels na jarumai da yan kasuwa shi ma za'a iya kalla anan haka dai da sauran su.
Akwai cigaba da nake so na gani da yawa a Masana'antar Kannywood wasu daga ciki sune.- mu kara rike sirrin junan mu. Bakomai ba ne za mu fito mu bayyana a soshiyal midiya, rayuwa sai da hakuri, zo mu zauna zo mu saba ne, saboda ba komai ba ne ya ke kara zubar mana da mutunci irin abin da wasu daga cikin Jarumai yan uwana suke yi a soshiyal midiya Sai kaga mutun ya fito yana zage-zage ya na cin mutuncin dan uwanshi a midiya”.
Ya kammala da cewa “kada mu manta muna da mabiya, muna da masu kallon mu kuma muna da iyaye sun bamu tarbiyya, irin wadannan su ne su ke taba masana'antar mu kuma Insha Allah muna fata da kokarin mu ga mun kauda su a Kannywood”.
©HausaLoaded
Post a Comment