Martanin Abdulamart mai Kwashewa kenan da yayi akan taimakon da yayi wanda a cikin jawabinsa yayi nuna ya wadanda na nuna hassada da wannan alkhairi da jarumin yayi.

Ga abinda wannan daraktan ko furodusa  ke cewa

"Salam ‘yan uwa,
An kwana biyu ana muhawara akan taimako da Adamu yayi. Ina so na janyo hankalinmu akan mu guji yiwa Allah shisshigi. Duk wani abin kirki Allah ake nufa da shi haka zalika duk wani abu maras kyau Allah ake sabawa. Allah kadai yake karbar aiki ba wani ba kuma Allah ne kadai yake yafewa wa’anda suka saba masa. Saboda haka domin me zamu zauna muna yanke hukuncin abinda Allah ne kadai masaninsa. Mu a matsayinmu dacewa yayi mu yiwa junanmu kyakkyawan zato na alheri. Kofa niyyar aikata alheri kayi sai Allah ya baka lada ballantana ka aikata ko kuma ka zama silar aikata alherin. A ganina ko Adamu ya bayar ko shine ya samar da hanyar da aka bayar ko amfani da shi akayi wajen bayarwa duk daya ne - aikin alheri ne. Mu kuma sai muyi himma mu dabbaka irin wa’annan ayyukan amma domin Allah. Allah ya sakawa duk wa’anda suke cikin wannan taimako, mu kuma Allah ya bamu ikon yin abinda ya fi haka."

View this post on Instagram

Salam ‘yan uwa, An kwana biyu ana muhawara akan taimako da Adamu yayi. Ina so na janyo hankalinmu akan mu guji yiwa Allah shisshigi. Duk wani abin kirki Allah ake nufa da shi haka zalika duk wani abu maras kyau Allah ake sabawa. Allah kadai yake karbar aiki ba wani ba kuma Allah ne kadai yake yafewa wa’anda suka saba masa. Saboda haka domin me zamu zauna muna yanke hukuncin abinda Allah ne kadai masaninsa. Mu a matsayinmu dacewa yayi mu yiwa junanmu kyakkyawan zato na alheri. Kofa niyyar aikata alheri kayi sai Allah ya baka lada ballantana ka aikata ko kuma ka zama silar aikata alherin. A ganina ko Adamu ya bayar ko shine ya samar da hanyar da aka bayar ko amfani da shi akayi wajen bayarwa duk daya ne - aikin alheri ne. Mu kuma sai muyi himma mu dabbaka irin wa’annan ayyukan amma domin Allah. Allah ya sakawa duk wa’anda suke cikin wannan taimako, mu kuma Allah ya bamu ikon yin abinda ya fi haka.
A post shared by Abdul Amart Muhammed (@abdulamart_mai_kwashewa) on


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top