yadda zaki gane kin sami juna 2 a watan farko zuwa na 2.

Shi juna 2 al amarina babba daga cikin baiwar ubangiji danhaka kowacce mace ita kadai tasan yadda takeji ji idan tasami juna 2 domin akan sami wasu alamomin agun wasu matan wasu nasu alamomin sukan banbanta dana wata matar ,yadangan ta da lafiyar mace,kwayannin halittarta.wadatar abunci me gina jiki ,DAKUMA YADDA TAKE TAFIYAR DA TSARIN RAYUWARTA.

Duk dahaka akwai alamomi da suke kusan kowacce mace idan tasami juna biyu to dole tajisu daga wata 1 zuwa 2 na junan biyun.
Wadannan sune alamomin juna biyu nafarko.

*YANAYIN MAMA KAN DAN CANJA KODA KADANNE.*

wato nonuwanta kan dan ciko yaqaru imma kadan ko dayawa ,asakamakon canjawar sanadarai koda a wata na 1 ne.

*2 saurin jin fitsari fiye da yadda akasaba ji alokutan da babu juna
wato koda fitsarin bai qaruba zatana jin mafitsararta kamar akwai fitsari haka zuwa bandakinta zai qaru akan nada kadan koda yawa kuma koda intaje bazaitai komaiaba.HAKA ZATAI TA JI HAR WATANNIN HAIHUWARTA HAKA ABUN ZAITA QARUWA.

*3 batan wata: wato idan mace yazamana wata yakama yamutu lokacin al:adarta yazo yawuce amma bata yiba kuma qalau take bakuma magungunan tsarin iyalitake shaba to itama wannan babbar alamace dake nuna mace tasami juna 2.

4*Canjawar yanayin jiki wato tamfirica : yakan dan canja kadan wata taji kasala jikinta jum kamar tagaji .amma wasu basajin hakan.

5* yawaitar ji kamar za ayi amai dakuma saurin yin amai musamman in anji wari ko qamshin abun da rai bayaso.

*6 kyamar wani nau'in abunci dakuma son wasu abuncin nadaban IDAN AKWAI QARANCIN JINI AJIKINTA MACE TAKANYI KWADAYI DA SON ABUNDA BA MA ABUNCE BA KAMAR GORUBA ,WARIN WANI ABUN,FARAR QASA,QASA ,manja warin bandaki ,ruwan koji dadai shauran su.

Dazarar anga haka to ana so abawa mace kulawa ta musamman,

* yimata gwajin fitsari dan tabbatar da samuwar juna biyun.

* fara zuwa awun ciki

* bata abunci me kyau da gina jiki.
* kareta daga cututtuka masu illata mejuna biyu kamar maleriya,

*kula da hawan jinin jikinta ko saukarsa.
* kula da jikinta shin jini yaimataa qaranci koko a a.

* yanayin cikin yana girma lafiya koko akwai matsala.
* dadai shauran su


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top