Shafin aminiyahausa ya wallafa.
 A tsakiya Darakta Sunusi Oscar da jarumi Garzali Miko a dama da Alhaji Sheshe
Sunusi Oscar 442 fitaccen darakta ne da ke jan zarensa a Kannywood, musamman yadda masu kallon fina-finan Hausa suke son kallon fina-finansa. A tattaunawarsa da Aminiya, daraktan wanda ake yi wa lakabi da Kwankwason Kannywood ko Mai Daraja, ya bayyana yadda ya shiga harkar da yadda ya shigo da sababbin jarumai da kuma kama shi da Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta yi a kwanakin baya:

Mene ne takaitaccen tarihika?

ADVERTISEMENT
Sunana Sunusi Hafiz, wanda aki sani da Oscar. An haife ni a Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano. Na yi makantar firamare da sakandare duk a Fagge, na yi karatun addini bakin gwargwado. Na taso cikin maraici domin ina karami mahaifina ya rasu. Wannan ya sa aka shiga cikin gwagwarmayar rayuwa har daga baya na shigo Masana’antar Kannywood.

Na samu sunan Oscar 442 ne a kwallon kafa. Domin ban taba tunanin ba zan ci abinci a kwallon kafa ba. Amma cikin ikon Allah sai ga ni a Kannywood ina cin abinci. Komai nawa fim ne a yanzu, kuma ina godiya ga Allah.

ADVERTISEMENT
Yaya aka yi ka tsinci kanka a Masana’antar Kannywood?

Kusan shekara 25 ko sama da haka, na kasance ma’abucin son kallon dirama ta dabe. A unguwar da muke ana irin wannan dirama, hakan ya sa muke zuwa kallo idan mun tashi daga makaranta. Daga nan sai muke ganin duk da cewa muna yara amma akwai kuskure a ciki, daga haka muka fara ba da shawara. Daga nan har muka kai ga karbar shugabancin wajen. Wannan ya sa na ga ya kamata mu ci gaba daga inda muka tsaya domin mu fadada sakon da muke isarwa don duniya ta shaida. Sai muka yi shawarar yin fim, sai ya kasance wadanda muke tare da su ba za su iya daukar nauyi ba, sai na dauki nauyi, kuma na fito a jarumi. Kuma cikin ikon Allah aka samu nasara a wannan fim din. Wannan shi ne yadda aka faro.

Me ya sa ka zabi ka zama darakta?

Na fara fim a matsayin mai shirya fim ne, sai na ga irin kura-kuren da ake yi, wannan ya ba ni sha’awar in fara ba da umarni, kuma na gwada na samu nasara. Domin tunda na fara aikina zuwa yanzu, ban taba samun wani kalubale ba na wani abokin aikina ya ce bai yi masa ba, ko dan kallo ya ce bai yi masa ba. Da a ce na samu wani kalubale cewa bai yi ba, da na ajiye bangaren domin masa’antar tana da fadi.

Wane fim ka fara ba da umarni?

Fim din da na fara shi ne ‘Abin Da Ka Shuka’, kusan shekara 23 ko 24 da suka wuce ke nan.

Mene ne burinka a bangaren ba da umarni?

Burina a bangaren ba da umarni shi ne wata rana in zama darakta a Nollywood ko Bollywood. Wato a kullum ba na kallon kaina a matsayin wanda zai kare rayuwarsa a Kannywood, kullum tunanina shi ne yadda zan ci gaba.

Ana alkanta ka da Tamil Nadu, masu karatu za su sanin mene ne wannan?

Tamil Nadu wata jiha ce a Kudancin Indiya kuma suna da masana’antarsu mai zaman kanta. Abin da ya sa muke lakabi da ita shi ne kasancewar mutane ne masu basira da labarai masu ma’ana, amma saboda an fi sanin bangaren Bollywood na cikin Indiya, sai ba a san da su ba. Kuma akasari ma labarinsu ake dauka a yi amfani da su a Indiya kuma a yi nasara. Wannan ya sa saboda mu din ma da mutanenmu ba su fahimce mu ba, kuma ba cika baki ba, ga shi yanzu mun iya, kuma muna kawo yara wadanda suka kware, muna kuma kawo abubuwan zamani. Ka ji abin da ya sa muke kiran kanmu Tamil Nadu. Yanzu yaran da muka koyar su ne suke jan ragamar Kannywood.

Yaya alakarka da sauran ’yan fim?

Alakata da sauran ’yan fim alaka ce mai kyau musamman masu son ci gaban Kannywood. Idan ka ga muna rigima da wadansu a masana’antar to mutane masu son dunkusar da ita ce amma mutane ba su san su ba. Ba za mu zauna mu zuba ido muna kallo a bata mana masana’anta mu yi shiru ba. Amma a cikin kashi 100, muna da alaka da mai kyau da kashi 85. Ka ga kuwa muna da alaka mai kyau ke nan. Kashi 15 din su ne fitinannun, kuma da sannu za mu sanar da duniya halin da ake ciki a kansu. Abin da suke yi daban, Kann

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top