'Yar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari a ranar Juma'a ta bawa al'umma mamaki yayin wani taro da BBC Hausa ta shirya inda ta bayyana cewa ba ta iya magana da harshen Hausa sosai ba duk da cewa mahaifinta bahaushe ne.

An shirya bikin ne don karrama zakarru a wata gasar rubutun harshen hausa da BBC Hausa ta shirya.

Shugaba Buhari bahaushe ne daga daya daga cikin garurruwa masu muhimmanci a tarihin hausa wato Daura a jihar Katsina. Mahaifiyar Zahra, Aisha kuma bafulatana ce daga jihar Adamawa.

A lokacin da aka bukaci Zahra ta yi jawabi a wurin taron da ake gabatarwa da harshen Hausa, ta ce, "Zan baku dariya."




Ta ce ita da sauran 'yan uwan ta ba su cika magana da harshen hausa ba.

Cikin dariya Zahra ta ce, "Mahaifi na ya kan ci gyara na duk lokacin da muke magana da harshen Hausa."

Ta ce sun fi magana ne da 'Engausa' ma'ana wata harshe da mutane suka kirkira da cakwuda Hausa da Turanci.

Ta ce dalilin da yasa ba ta koyi harshen Hausa ba kamar yadda ya kamata ba shine domin a lokacin da ta ke zuwa makaranta galibin daliban 'ya'yan turawa ne.

Daga bisani diyar shugaban kasar ta shaidawa manema labarai cewa sun fi amfani da harshen mahaifiyarta wato Fulfulde wurin yin magana a gida

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top