A jiya, gwamnatin kasar ta bayyana cewa ya zama dole a buda wuta wajen neman kudi ta sauran hanyoyin duk da za a same su idan har ana so a cin ma burin da ke cikin kundin kasafin badi.
Zainab Shamsuna Ahmed ta kyankyasa wannan ne a lokacin da ta kare kasafin kudinta Ranar 23 ga Oktoba a gaban majalisar wakilai a Abuja inda tace su na neman kudi a wajen man fetur.
Shamsuna Ahmed ta na cewa: “Mu na fama ne da matsalar samun kudin shiga; kokarin tatsar kudinmu 58% ne rak. Don haka mu ka tsara hanyar kara samun kudi a farkon shekarar nan .”
Babbar Ministar kudi da kasafin kasar tace dole a yi garambawul a game da yadda gwamnatin tarayya za ta rika samun wasu kudi daban da ba ta bangaren mai ba, inda ta tabo batun aron kudi.
“Akwai bukatar mu samu damar inganta samun kudin shiganmu. A matsayinmu na kasa, dole Najeriya ta samu dukiyar da za ta gina abubuwan more rayuwa da ayyukan a zo–a gani. ” Inji ta.
A cewar Ministar abin da Najeriya ta ke samu na kudin shiga kashi 8% ne na jimillar karfin arzikinta na GDP. Haka zalika duk bashin da Najeriya ta ke ci, bai kai 50% na arzikin kasar ba.
Daily Trust ta rahoto cewa wasu Sanatoci su na ganin bai kamata gwamnati ta cigaba da neman aron kudi ba. Ministar kudin kuwa ta na ganin har yanzu ba ta haura malejin cin bashin na ta ba.
Mun samu wannan bayyani daga shafin Nijeriyarmu a yau a facebook
©HausaLoaded
Post a Comment