![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgJPxmRhqQNwMb_wHN0MoQO6fekEMk2BGSt7paYVef3W2FK9CZPVQcKI1ZDtHqJadyql2fLpT1BoBYP2im8yuwqT8Jh3vbdvkFaqIK_C0FXfQWnInWvY3Zc9CasOz30TWVUI5VmjBJwaH40/s1600/6935811245nstagramfark.jpg)
A Holan,yayin da suke kokarin ceto ranta,wacce mace da ke cikin mawuyacin hali sakamakon wani kazamin hatsarin da ta yi,ta roki jami'an agaji da su dau hotonta tare yada shi a shafinta na sada zumunta na Instagram,saboda hakan zai matukar birge masoyanta.
Wannan lamarin dai ya afku ne a ranar Alhamis din nan da ta gabata a garin Zaanstreek na yankin Amsterdam,inda babur din da ke dauke da wata mace mai tallar madara ya yi taho mu-gama da wata mota.
A cewar labaran da aka rawaito daga yankin lamarin ya afku,a daidai lokacin da jami'an agaji ke kokarin ceto ranta,macen wacce ke a cikin mayuwacin hali,ta yi ta nanata bukatarta na dau hotonta tare da yada shi a shafinta na sada zumunta na Instragam,saboda hakan zai sa ta samu dubun dubatan "Like".Amma suka ki amince da bukatarta.
An bada cikakken bayani kan wannan lamarin a shafin sada zumunta na Facebook na 'yan sandan a wani labari mai taken "Duniyarmu ta haukace",inda kakakin 'yan sandan yankin Zaanstreek ya ce :
"Na daina mamakin irin wadannan ababen.A gaskiya muna rayuwa a wata duniya mai ban ta'ajibi".
Post a Comment