Aikin Dan Sanda aiki ne na kare lafiyar alumma da dukiyoyinsu a cikin alumma. Suna cikin alumma a koda yaushe shi yasa ake musu lakabi da "Dan sanda abokin kowa".
Suna gudanar da ayyukansu cikin hikima da dubaru wajen tuhumar wanda ake zargi da aikata laifi.
Aikin Dan sanda aiki ne mai kyau matuka wajen tabbatar da zaman lapia a cikin alumma da kuma kare lafiyarsu da kuma dukiyoyinsu.
Gwamnati tana kokari wajen ganin ta kyautata rayuwar jamian Yansanda ta hanyar biyansu hakkokin albashinsu akan kari da kuma inganta albashin.
Nan baya kadan Marigayi tsohon shugaban kasa Umar Musa Yaradua ya kara ma hukumar yawan albashi don kyautata rayuwarsu. Sannan a yanzu haka shugaban kasa Buhari ya bada umarnin kara musu albashi.
Sai dai dayan bangaren wasu daga cikin jamian nan suna amfani da damar aikinsu wajen amsar cin hanci da rashawa tituna, kotuna da ofisoshin su yayin tuhumar masu laifi da amsar beli. Bugu da kari wasu bara-gurbin shugbanni suna amfani da wasu bara-gurbin jamian tsaro wajen cin ma wasu bukatu, ta hanyar amfani da yan bangar siyasa da sauransu. Dilolin Yan kwaya suma suna amfani da wasu damarmaki wajen aikata ayyukansu.
Wannan tasa da yawa daga cikin mutane a cikin alumma suke yi ma aikin Yansanda ganin gurbataccen aiki ne, wanda yake cike da zalunci da cin hanci da rashawa a cikinsa.
Suna yi ma maaikatar kallon wata mafakar shugabanni da masu kudi da duk wani maras gaskia a lokacinda suka aikata laifi.
Bayyanar Kwamishinan Yan sanda Na Jihar Kano Muhammad Wakili ya canza tunanin mafi yawan alumma akan aikin Yan sanda. Kama daga yaki Yan kwaya musamman Dilolinsu yana kama su yana daurewa, yana tuhumarsu don gyara tarbiyyar alumma.
Bugu da kari, Wakili yayi suna wajen yaki da Bangar siyasa wajen kame su ya hukunta su tare da kame iyayen gidansu na siyasa da suke saka su aikata munanan ayyukan.
Wannan irin jajircewa ta yaki da munanan ayyuka shine yasa Alumma suke yi masa lakabi da "Singham" (sunan da suka samo a wani film din India da wani jarumin Dansanda yayi yaki da taaddanci da miyagun mutane).
Jajircewar CP Singham a Kano wajen yaki da Rashin gaskia har abinda ya kawo lokacin zabe inda ya kama wasu manyan gwamnatin jihar Kano yayi matukar kara masa suna da masoya da kuma son aikin Dansanda din gaba daya.
Ganin irin tasirin aikin Dansanda daga wajen Wakili yasa Mutane da yawa suka tsunduma son aikin don taimaka ma al'ummarsu da kasa baki daya.
Rariya.
Post a Comment