Cigaba daga makon jiya

Daga nan fa Abdurrahman ya zamo cikakken sarki, ya naɗa gwamna a Seɓilla, sannan ya fara shirin yadda zai karɓe ikon sauran garuruwan masarautar waɗanda gwamnoninsu suke biyayya ga tsohon Sarki Yusuf Al-fihiri, kamar garuruwan Zaragoza, da Toledo, da Barcelona da wasunsu. Bayan an yi haka ne, sai Sarki Abdurrahman ya faɗa wa duniya cewa Umayyad ta Damaskus ta dawo Andalus, watau kamar canjin waje ta samu daga Damascus zuwa Andalus, shi ne kuma ya aika wa duk wani ba Ummiye cewa ya dawo masarautarsa da zama. Nan da nan kuwa jinsin ƙuraishawa suka rinƙa turereniya zuwa garin tunda daman Abbasiyawa sun tarwatsa su sun watsu a duniya, a lokacin ne ‘yan uwansa mata suka zo garin ƙordoba tare da ɗansa Sulaiman wanda rabon da ya gan su tun a yankin Tekun Yufrates sa’ilin nda ya gudu ya bar su suna kuka.

Abdurrahman ya rinƙa naɗa ‘yan uwansa Umayyawa a manyan muƙamai, saboda a cewarsa za su fi zamowa masu aminci a gare shi fiye da kowa. A shekara ta 763 ne kuma aka ci gaba da fafatawa. Sarkin Daular Abbasiyawa wadda ta tashi daga Damaskus zuwa Baghdad mai suna Al’mansur ya turo gwamnan Afirka mai zama a
Kai rawani mai suna Al’ala Ibn Mugith don ya halaka Abdurrahman ya kuma ɗora wa Andalus sabon sarki. Ai kuwa Sarki A’ala ya sauka a wani waje da ake kira Beja, wanda aka ce a yanzu yana yankin ƙasar Portugal ne, a tare da shi akwai sadaukai kimanin dubu bakwai. Daga can ƙordoba, sai shi ma Sarki Abdurrahman ya yiwo hawa, ya nufo su domin a gwabza yaƙi. An ce a lokacin da Abdurrahman ya ji labarin
sadaukan Abbasiyawa sun isa wani waje mai suna Karmona inda suka yi kwanton ɓauna, ga shi ya baro gida babu wani isasshen guzuri na abinci ga mutanensa, sai ya tara mutanensa ya faɗa musu cewa lokacin da za su rinƙa jira ana kawo musu hari ya wuce, don haka a maimakon su rinƙa jiran mayaƙa su zo gare su har yunwa ta galabaitar da su, dole za su yi ƙarfin halin kai hari da kansu.

Shi ne sai ya zaɓi sadaukai masu iya faɓa guda ɗari bakwai, ya shige gaba suna biye da shi a baya har zuwa Karmona, sannan suka faɗa wa mayaƙan Abbasiyawa da yaƙi ba tare da sun yi tsammani ba. A wannan yaƙin Abdurrahman ya ci gagarumar nasara, har ma sai da ya datse kan Gwamna Al’ala ibn Mugith da wasu manyan kwamandojin
Abbasiyawa. Sai kawai aka sanya kawunansu cikin gishiri, aka tura wa Sarki Almansur da yake a garin Makka a lokacin da yake gudanar da aikin Hajji. An ce da ya gani sai ya yi ajiyar zuciya. Ya ce “Alhamdullahi, Allazi Ja’alal Bahru Bainana” (Ma’ana, godiya ta tabbata ga Allah da ya sanya akwai teku a tsakaninmu). 

Saboda ya tsorata, yana ganin da babu teku, Abdurrahman zai iya kawo hari ya kashe shi a duk
inda yake. Daga nan Al’mansur ya laƙaba wa Abdurrahman lambar girma ta “ƙasr ƙuraishin”.

A takaice dai, Sarki Abdurrahman ya yi yaƙe-yaƙe da dama. Ya yi niyyar zuwa Baghadad domin ɗaukar fansa, amma ya fasa saboda rikicin cikin gida da ya dame shi. Domin kuwa ya rinƙa samun ‘yan tawaye a mulkinsa masu yi masa bore, sai ya yaƙe su ya ci nasara. Haka kuma ya yi yaƙi da garuruwan da ke masarautarsa har sai da ya
tabbatar ya karɓe mulkin yawa-yawansu, sannan kuma ya yi yaƙi da ‘yan ƙabilarsa Umayyawa masu neman kashe shi don su hau kan sarauta. A ƙarshe, Sarki Abdurrahman ya gina babban masallacin da ya yi suna a duniya a garin ƙordoba, ya kuma shirya rundunar sojinsa da dakaru kimanin dubu arba’in. Ya rasu a wajajen shekara ta 788, ɗansa Hisham ne ya gaje shi, ɗansa Sulaiman kuwa ya naɗa Gwamnan Toledo tun yana da rai lokacin da ya ƙwato garin, kodayake, an ce bayan rasuwar Uban, sai da Sulaimain ya yaƙi Hisam, har kuma Hisham ɗin ya yi masa hukuncin ɗauri a shekara ta 800. Amma dai bai kashe shi ba.

Masarautar Andalus ta Musulunci, masarauta ce ta ilimi, wadda manyan masana suka rayu a ƙarƙashinta, kuma ta wanzu kusan shekaru ɗari bakwai tana mulki, domin kuwa lissafin zai faro ne tun daga shekarar 711 har zuwa shekara ta 1490, sa’ilin da Sarki Muhammad ɗII ya yi sulhu da Kiristoci abokan hamayyarsa, watau Sarki Ferdinan II na Argon da kuma Sarauniya Isabella ta Castle.

A nan mu kawo ƙarshen wannan tarihi. Alhamdulillah


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top