✿••HANYOYIN DA ZAKI BI KI DINGA GAMSAR DA MIJINKI A SHIMFIDA••✿

wannan babin yana da matukar muhimmancin kwarai da gaske, domin yawancin matsalar ma'aurata tana faruwa ne daga gurin kwanciya ,yawan korafi da koke-koke da mata ke kawo wa a kan wannan matsala.

Domin yawancin mata suna yawan kawo karar mazajensu suna wulakanta su, ba su damu ba su ba, ba sa dauke musu bukatarsu, wasu matan ma cewa suke sai su yi wata mazajen nasu basu kusance su ba, wasu kuma cewa suke mazajensu ba sa kula da su wulakanta su suke ko su ce sunfi nan nan da kishiyoyinsu.

      ヘ ̄GAMSAR DA SU ̄ヘ

Akwai matan da suke fadin karara mazajensu suke fitowa suke gaya musu cewar kishiyoyinsu sun fi gamsar da su, sunfi su iya kwanciya.

Ni ina ganin dan miji ya gaya miki haka ba cin fuska bane so yake ki gyara dan yawancin maza basu da rufi, to ke kuwa idan miji ya gaya miki haka mai zai sa ba Zaki dage ma ki koyi salo-salo da hanyoyin kyautatawa miji yayin kwanciyar ba.

Ki tuna fa mijinki duk abin da kike yi masa na kyautatawa ba ki da laifi, sai riba da lada tsababa gurin ubangiji.

Dan haka ki kiyaye wadannan abubuwan da Neman zama yar mowa idan har kina yi to kin yi adabo da boranci.

Ki kasance mai kyautatawa mijinki da yin duk wani abu da kika San idan kinyi zai faranta masa rai, na zamantakewar gida sannan ki tabbatar kin kyautata masa hanyar abinci, wato yi masa duk wani kalar girki da kika San yana sha'awa kuma yana burge shi.

       ⊂ ̄•••TURAKA••• ̄⊃

♡ ki tabbatar kin tsabtace jikinki ta hanyar yin wanka, wanke baki da sauransu kafin ki isa shimfidar da za ku kwanta da maigida idan da dama kina iya saka cingam 🍬 mai kamshi ko alewa 🍫a bakinki.

♡ ki tabbatar kin shafe jikinki da turaruka masu sanyin kamshi da dadi sossai, kamar humra mai kamshi da Kama jiki, shafa man hammata , fesa turaren jiki a dukkan jikinki da feshe rigar baccinki ko zanin da Zaki daura da turare mai kamshi Jan hankali kamar su: 

→ touch me
→ new musk
→ dial
→ far away da sauransu.

♡ ki tabbatar kin cire duk wani abu da yake na karfe a jikinki kamar 

→ yari
→ sarka
→ zobe
→ awarwaro da ribon

Sannan karki saka kaya mai nauyi , kuma matsasu ko wandanda zasu yi wuyar cirewa a jikinki.

♡ ki tabbatar kin cire duk wata damuwa da bacin rai daga zuciyar ki kafin ki kwanta.

♡ ki tabbatar kin tanadi mifici dan yiwa mai gida fifita yayin da kuka kwanta ko kuma yayin da ya hada gumi lokacin daya gama kusantarki baranma idan ba wuta 💡ma'Ana ba fanka ko AC.

♡ sannan ki tanadi toilet paper ko wani hankici mai tsafta dan gogewa mai gida gumi lokacin da yake kusantarki.

♡ ki tabbatar kin isah shimfidar da maigida yake kwance cikin fara'a da walwala.

♡ kar ki yadda ki kawo masa maganar da za ta bata masa rai a lokacin bacci, kuma ko da shi ne zai yi miki korafi a kan yi masa wani abu ko wani ya bata masa rai ki tabbatar kin rarrashe shi da kwantar masa da hankali ta hanyar maganganun da kika San zasu saka shi ya samu nutsuwar zuciya.

◇ idan kin Riga maigida zuwa shimfida kar ki juya masa baya Inda ya kwanta bayanki zai dinga gani ki kalli Inda zai fuskance ki tunda ba kullum mijinki zai kusance ki ba dan sha'awa zuwa zuwa ce, wata Rana zaku kasance ba ya sha'awar ki ba kya sha'awarsa wata ran kuma sai Ku kwana bakwai kuna yi dan haka duk sanda kuka kwanta kar ki juyawa maigida baya sai kin tambaye shi baya bukatarki cikin wasa.

◇ karki zama dosoruwar mace kullum sai mijinki ya neme ki ko ya taba ki sannan Zaki Fara taba shi, ya dace wani lokacin ki Fara nuna masa sha'awarki kafin ya nuna miki ta hanyar rike masa hannu, shafa shi , rumgume shi, da yi masa wasa da 'yan zantuttuka tada sha"awa.

◇ ki zama mai juriya da daukan duk wani abu da yayi miki ko kuma yazo miki da shi lokacin da yake kusantarki karki yadda ki nuna masa ragwantarki da kosawarki a lokacin.

◇ ki taimaka masa idan kin fahimci yana bukatar taimakonki a lokacin da yake kusantarki ta kowace siga in dai bai kaucewa shari'ah ba.

◇ kiyi kokarin nuna masa cewa ke ma kina bukatar sa kuma kina kaunar sa ta hanyar yi masa duk wani abu da kika San zai tabbatar masa da hakan yayin da yake kusantarki.

◇ karki cuci kanki kiyi kokarin nuna masa ko gaya masa abinda zai yi miki dan ki sami gamsuwa, ko da kuwa nuna Masan ne da hannunki.

◇ karki yadda kuyi amfani da tsumman goge al'aura ko takardan goge datti ( toilet paper) guda daya lokacin daya gama kusantarki an ce yana janyo tsana a tsakanin ma'aurata.

◉ ko da kun goge gabanku bayan gama jima'i idan ba za Ku yi wanka a lokacin ba to kiyi kokarin zuwa kiyi tsarki ki wanke gabanki sossai, idan ba kya wanke gabanki bayan saduwa Zaki iya gamuwa da cutar daukewar sha'awa ko kuma ta kaikaiyin gaba, 

manzo Allah ( S.A.W) yace Ayi alwala Inda ba zaku iya wanka ba.

◉ karki juyawa maigidanki baya bayan gama kusantarki idan da hali ma Zaki iya rumgume shi kuyi bacci a haka.

🎙ya yar'uwa idan kika yi riko da yin wa'yanna abubuwan a turaka to ina tabbatar miki da cewa sai dai Ku goge kafada da kafada da kishiya ko ma kifi ta dan maigidanki zai daina yi miki korafin cewar ba kya gamsar da shi sossai, kuma zaifi nuna sha'awar ki da yawan kusantar ki akai-akai.

╥╥LARURAR RAGE ARMASHIN SADUWA╥╥

Sai dai akwai wasu matan da duk abinda suka yi wa mazajensu a shimfida dan su gamsar da su to ba zasu gamsar da su din ba domin larurar da take jikin matan.

| KAR KI BARI A BARKI A BAYA BAKI KARANTA BA |


ZABI DA KANKI KI GYARA DA KANKI

¹ misali : wata matar zaka ji tana cewa ita ko yaushe gabanta a bushe yake kuma ko da mijinta yana kusantarta a bushe gabanta yake kandas, to kun ga matar da take da wannan matsalar mijinta ba zai dinga gamsuwa da ita yadda ya kamata ba, ita kuma ba zata taba jin dadin saduwar ba, sai dai ma ta dinga jin zafi , bayan an gama kusantar ta gabanta yayi ta radadi.

Irin wadannan matan kusan duk abinda zasu yi ba sa burge mazajensu, domin rashin ni'imtuwa da su da ba sa yi sai dai su zauna da su dan ba yadda zasu yi dasu , idan kuwa mace tana da kishiya sai ki ga ran girkin kishiyar yana rawar kafa dare yana yi ko kofar gida ba zai fita hirar ba zai shige daki ba Zaki kuma ganinsa ba sai da safe.

RASHIN NI'IMA GA "YA MACE YA KASU KASHI BIYU AKWAI NA HALITTA AKWAI KUMA NA LALURA.

□•••⚀ na halitta shine wanda dama ita macen haka take kuma haka halitarta take Sam ba ta da ni'ima.

Kuma irin wa'yanna matan zaka ji suna cewa su ba su San dadin namiji ba Sam.

Abin mamaki kuma a haka zaku ga suna hayayyafa.

To yar'uwa ko da kina cikin jerin wayannan matan karki zauna kice ba abinda Zaki yi dan haka halitarki take, a'a sai ki dukufa Neman magani amma babban abinda Zaki fi mai da hankali akai shine cin duk wani abu ko sha na ni'ima.

🍏🍎🍐🍊🍋🍌🍉🍇🍓🍈🍒🍑🍍🍅🍅🍆🌶🌽🍠🍤.

◇ na lalura kuwa shine wanda ni'imar mace take daukewa yayin da ta haihu ko idan lalurar 
••| KURAJE KO KAIKAYIN GABA KO RASHIN CIN ABINCI |••

da ya dace ta dinga ci a matsayin abincin ko sha ko ciwon basir ko tsannanin kazanta da rashin tsaftace gaban, kamar lokacin jinin al'ada, da bayan gama jima'i sannan da rashin tsaftace bandaki ko shiga bandakin taraya 🕳 ba tare da an tsaftace shi ba, ko shafar aljanu da sauransu.

Amma daukewar ni'ima na lalura ba wani abu da za'a ce mace taci ko ta sha dan su saukar mata da ni'ima, idan ko taci ko ta sha ni'imar ba zata samu ba har sai tayi maganin lalurar da take tare da ita, ta warke sannan zata Fara ci da shan kayan saukar da ni'ima idan kuwa ta warke to tana Fara ci ko shan ni'imar tata zata dawo, wata kila ma har Tafi ta da, dan haka kina ganin kin gamu da daya daga cikin wa'yanna lalurori dana lissafa sai ki garzaya zuwa 

ISLAMIC MEDICAL CENTER

  ••••| BASIR GA "YA MACE |••••

> basir na daurewar ciki - ta yawaita cin ya'yan itatuwa kamar lemon 🍋 Zaki taci har dusa da fatar ciki.

> shan kankana 🍉 ta dinga taunewa har kwallon ciki.

> cin ganyen salad bayan ta warke soaai ta yanka tumatur 🍅 da yawa ta sa gishiri da magi da mai kadan ciki.

> yanka ganyen kabeji kina kwadawa kina ci ko ki zuba a kan abinci.

> yin miyar alayahu ko shuwaka ko ugu amma ta zuba ganyen da yawa a ciki.

> cin ganyen zogale 🌿 ko rama 🍃 ko dinkin ko yadiya ko lamsir amma kar ta cika kuli-kuli da yawa a ciki.

> yawan shan ruwa sossai.

Ya dace kullum kici Kala daya ko biyu daga wannan abubuwan Dana lissafo.

○BASIR MAI TSURO KO MAI BURTSOWA SAI AN MAYAR DA HANNU KO MAI ZUBAR DA JINI○

¶ ki tafasa makuba da gishiri a ciki ki tace ki shiga ruwan da dumi ki zauna a ciki kamar Rabin awa, a kalla kiyi sau biyu a Rana.

¶ ki tafasa sassaken mangwaro da jar kanwa ki dinga sha.

¶ ki daka citta tayi laushi, dakakken garin bakar habbatussauda ki kwaba da zaitun ko zuma ki dinga matsawa a duburar.

¶ ko ki Tafi hospital dan wani basir din sai anyi aikin.

■•••••SHAFAR ALJANNU•••••■ 

∆ ki kasance duk sanda Zaki kwanta ki dinga daura alwala.

∆ ki yawaita yin istigfari hailala da salatin annabi ( S A W) 

∆ ki karkade shimfidar kafin ki kwanta sannan ki karanta ayatul kursiyyu da falaki da nas.

∆ ki kwanta da barin hannunki na dama kiyi ta maimaita ayatul kursiyyu har bacci.

SINADARAN TABBATUWAR NI'IMA DA ZAMA CIKAKKIYAR MOWAR GIDA.

= BUSASSHIYAR MACE:

¶ sassaken baure.
¶ ruwan rake.
¶ ya'yan zogale.
¶ ruwan zuma.
¶ ruwan dabino.

Ki daka sassaken baure ko ki barshi a sassaken sa, ki zuba ruwa cikin kofi daya, mai girman ( jug ) idan gari ne sai ki sa cokali biyar idan sassaken ne sai ki kintata kamar yadda idan kin daka zai ba ki cokali biyar din, ki Dora a wuta ya tafasa kamar awa guda, sannan ki sauke idan ya kwanta sai ki tace, sai ki zuba markadadden ruwan kankana kofi daya, ruwan rake ma kofi daya ruwan dabino ma kofi daya, zuma Rabin kofi garin ganyen zogale cokali biyu, sai ki Dora a kan wuta Yayi ta dahuwa sai ya dahu sosai , zai yi kauri amma ba kirtif ba, idan ya huce sai ki dinga shan Rabin kofi safe da yamma Zaki ban labari.

◇DAUKEWAR NI'IMA BAYAN HAIHUWA◇

🍉 sassaken kankana.
🌿 sassaken baure.
🍃 ya'yan zogale.
→ idon zakara.
→ asuwaki mata.
→ ganyen kafi suga.

Ki hada ki dake ki tankade yayi laushi sossai ki dinga zuba cikin cokali abinci daya cikin madara shanu kofi daya ko cikin madarar ruwa gwangwani daya kina sha safe da yamma.

GYARAN JIKINMU TA KO INA YADDA ZAKI DINGA KYALLI.

MAGANIN KURAJE DA KYAU FUSKA.

∩••••••SABULUN KURAJE••••••∩

→ asef soap.
→ pharmaderlm soap.
→ kanwa.
→ jar dilka.
→ zuma.
→ lemon tsami

→ ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, ki kwaba dilka da ruwan zafi cikin cokalin cin abincin daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar ko bakwai kafin ki shiga wanka idan kin shiga wankan sai ki kuma wanke fuskar da sabulun kamar sau uku ko sama da haka insha Allah idan kina yi duk kurajen fuskarki zasu mutu.

SABULUN FIDDA TABO

¶ misscoroline soap
¶ shary soap
¶ aloebera soap
¶ garin alkama
¶ zuma
¶ kanwarki kadan
¶ lemon tsami bari

Sai ki goga su ki zuba zuma a ciki da lemon tsami da kanwar ki kwaba. Ki dinga shafawa a fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma Zaki yi wanka da shi Zaki dinga wanke fuskarki.

•••••••∆•LALLEN FUKSA•∆••••••••

✿ฺ lalle

✿ kurkum

ฺ✿ฺ sukari

✿ฺ dilak

✿ฺ Zuma.

Sai ki kwaba ki shasshafe fuskarki da shi, kamar minti uku sai ki yi ta murje fuskarki ki mutsutstsuke ta har kunnuwanki idsn lallen ya marmashe sai ki je ki wanke fuskarki yana sa kyan fuska santsi da kyallin fuska.

       ~~|•• LALAN JIKI ••|~~

••• lalle
•• zuma
• madarar gari
• dilka
• kurkum
• sukari
•mahala
• nescafe
• kaninfari

Ki hada ki kwaba da lallen ki shafe jikinki da ita ko ina ki mutittsike idan ta dan bushe ta marmashe sai ki shiga wanka, kiyi wanka da sabulun Dana koya miki shima lallen jikin yana da kyau sossai yana sa taushi da kyalli da santsin fata.

karin bayani
✆ WhatsApp 08037538596


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top