Assalamu alaikum ya ‘yan uwana mata. A koda yaushe Ina mai ƙoƙarin zaburar da mu game da tunasar da mu aikin da ke babanmu. Tabbas mu mata mu na da aiki a gabanmu. Kula d a al’amuran gida ba ƙaramin abu ba ne.

Kamar yadda mu ka gama yin bayanin yadda Uwargida ya kamata ta yi, to daren sanyin ma akwai yadda yakamata uwargida ta yi ta yadda za su ji daɗin bacci ita da maigida da iyali.

Uwargida ya na da kyau ki yi ƙoƙarin kammala abincin dare da wuri, kasancewar daren sanyi da wuri ya ke zuwa. Uwargida ki na kammala abinci, yi ƙoƙarin ɗora ruwan wanka. Idan kuma ku na da hita shikenan. Idan kuwa babu, sai ki ɗora ruwan wankanki, ki ɗora na maigida.

Ki na sauke ruwanki, sai ki shiga wanka. Ki na fitowa, sai ki sha ɗan ruwan ɗumi. Za ki ji daɗin jikinki. Daga nan sai ki shirya a nutse. Ki sami man shafawa mai danƙo ki shafa. Idan ki na da man kaɗanya, ki shafa, domin ya na ƙara laushin fata, ya hana jiki bushewa. Idan kuwa da hali, to sai ki tanadi man gilasirin. Sai ki ga jikinki ya yi laushi.

Kana ki shafa hoda kaɗan, kada ta yi yawa. Sai ki sa kwalli ki sa man leɓe, ki sami kaya masu kyau ki saka, ki sami rigar sanyi ki saka. Idan da yara, duka ki saka mu su kayan sanyi. Kana a shafe su da man zafi kafin ku kwanta.

Idan ku na da hita ta ɗaki, shikenan. Idan kuma babu hita, sai uwargida ta tanadi garwashin wuta ta zuba a kasko ta kai ɗakunan kwanciyarku. Amma za ki kai wutar kafin ku shiga kwanciya. Idan ɗakin ya ɗauki ɗumi sai ki fito da wutar ki kashe, domin kwanciya da wuta akwai hatsari, saboda lokacin sanyi, akwai iska.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top