Tambaya:

Assalmu alaikum, Allah ya kara ma malam lafiya da imani, malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna’i) a musulunci?
Amsa:

Wa alaikum assalam. To ‘yar’uwa Babu nassi ingantacce bayyananne yankakke da yake haramta wasa da al’aura har maniyyi ya fito, saidai wasu malaman sun haramta auran hannu saboda aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan bukatar sha’awa ta hanyar matar aure ko bayi kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba’a iya biyan bukata ta hanyar su.

Yin wasa da al’aura har maniyyi ya fita yana haddasa matsaloli a likitance, saidai yana daga cikin ka’idojin shari’a ; idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda za’a yi sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin da zai yi aure.

Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai barnar dake cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki, sannan tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za’a haifi ‘ya’ya gantalallu, marasa asali, wannan ya sa magana ta biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu sharudan da suka gabata.

Don neman Karin bayani duba: Muhallah 12\407 da Majmu’ul fataawaa 34\146>
Allah ne mafi sani.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top