Akwai matsalolin maza da yawa wanda yake haddasa rashin zaman lafiya a cikin aure ko kuma saki. Su ne kamar haka:

-Karya: Wasu mazan suna yi wa matayen da za su aura karya ta hanyar nuna masu cewa sun mallaki wani abun duniya wanda a zahiri kuma babu abin, ita kuma matar za ta soka tare da kwadayin samun wannan abun bayan an yi aure. Idan macen ta je gidan mijin kuma ta sami a kasin abin da yake fada mata to dole za su samu matsala wanda daga karshe dole za ta ce ya sake ta ko kuma su zauna cikin matsala kullum.

-Rashin Kulawa: Da yawa daga cikin maza na Hausa babsa kulawa da matansu, wanda ita kuma mace babu abin da take so sama da kulawa, idan har ya zama ba ka iya kulawa da bukatar matarka kamar abin da ya shafi abinci, sutura da sauran bukatunta, to dole za su sami matsala da mijinta wanda zai iya kawo rabuwarsu. Kulawa ta biyu kuwa ita ce, duk mace tana son a ce mijinta yana ba ta lokacinta wajen debe mata kewa, zama da ita domin jin ra’ayinta da kuma bukatunta, sannan kuma ka tabbatar mata cewa lallai kana sonta wanda hakan shima ya yi karanci a cikin maza. Wannan matsalace babba wanda rashin samun hakan yana kawo matsala sosai har a kai ga rabuwa.

– Rashin Tsafta: Duk mace tana son ta ga mijinta yana da tsafta da kuma kula da jikinshi, kamar yanda namiji yake so ya ga matarshi da tsafta kullum haka ita ma take so, amma za ka samu cewa hausawa da yawa ba su da tsafta, wasu kuma suna da ita amma ba su yi sai za su fita kasuwa ko aiki, ba dai a cikin gidansu ba, ba su yi don matansu wanda wannan shima yana kawo matsala ko kuma rabuwa.

– Cin Amana: Da yawa daga cikin maza suna ci amanar matansu ta hanyar neman matan banza wanda wasu lokutan sai ka samu cewa mace ta kama mijinta da matar banza ko a cikin gidanta ko kuma a waje wanda wannan yana kawo rabuwar aure.

– Zargi: Maza da yawa su kan yi zargin matansu a kan abin da ya zamanto su matan ba sa aikatawa, kamar neman maza, sata, ko makamancin haka wanda wannan shima yana raba aure sosai.

– Yin Aure Don Wani Dalilin Akasin Soyayya: Maza su kan yi aure don wani dalili na abin duniya, wasu mazan suna yin aure don kwadayin cewa
yarinyar mahaifinta yana da abun duniya, kuma ba za su sami dammar shiga cikin wannan abin duniyar ba har sai sun auri diya a gidan. Idan an yi auren ba su sami abin da suke za to ba, to sai su sake ta. Idan kuma sun samu to za a sami matsala har a yi saki saboda matar ta san cewa kudin babanta ne. Haka kuma wasu mazan su kan yi aure don yana yin sigar mace ko kuma sha’awa wanda idan tasami lokaci a wajen ka dole za ta canza shi kuma daga wannan lokacin zai ji baya son ganin ta saboda duk abubuwan da ke daukar hankali a tare da ita yanzu babu su, to sai su fara samun matsala wanda daga karshe sai saki.

-Matsalar Iyaye: A kasar hausa, iyayen su kan ba da matsala sosai a cikin aure, misali, za ka samu cewa da miji da mata suna son junansu, amma wani lokacin za ka ga iyayen mijin sun takura a kan cewa sai ya sake ta kuma ba tare da wata hujja ba wanda za a gamsu da ita, ko kuma su takura mata har daga karshe ta gaji ta ce ma mijin sai ya sake ta, ita ma kuma iyayenta suna iya sawa sai an sake ta saboda babu dalili.

-Matsalar Yan’uwa: Lokuta da yawa yan’uwan miji suna kawo matsala a aure, kamar takurawa macen, nuna mata kiyayya, yi mata sharri da sauran ire-iren wadannan wanda daga karshe sai ka ga sun rabu an kashe auren.

-Matsalar Abokai: Abokan miji suna ba da matsala a zaman aure wajen ba shi shawarar ban za ko kuma zuga a kanmatarsa wanda zai iya kawo saki, sannan kuma wasu mazan suna yin gasa cewa duk abin da suka ga matar wani aboki tana yi wa mijinta, to suma za su ce sai ta su ta yi masu irin shi wanda su kuma mata kowace da irin yanda take a wajen hali, halitta ko kuma ilimi.

Matsalolin Mutuwar Aure bangaren Mata
Mata suna da matsaloli da yawa wanda yake kawo masu rabuwar aurensu, daga cikin matsalolin ga wasu kamar haka:

-Kwadayi: Da yawa daga cikin mata su kan auri mutum don kwadayin wani abu da ke hannusa wannan abun shi ne dalilin da ya sa suka yi aure, bayan an yi aure sun je gidan mijin, za su tsaya su tabbatar da cewa wannan abun da suke so suna samun shi, idan kuma ya zama ba su samu ba, to za su ta da hankali a kan cewa sai an sake su, wasu kuwa ko da sun samu to duk sanda aka ce wannan abun babu shi ko kuma ya kare to haka suma zaman su da kai ya kare domin abin da ya kawo su ya kare. -Rashin Biyayya: Mata da yawa ba su da biyayya wanda shi kuma namiji yake bukata, sakamakon haka dolene aure ya rabu saboda rashin zaman lafiya.

– Rashin Iya Kwalliya, Abinci, Magana Da Kuma Tsafta Kwalliya : Rashin iya kwalliya da kuma ado yana kawo rabuwar aure, saboda shi namiji yana son ya ga matarsa cikin kwalliya a kowanne lokaci, za ka samu cewa miji ya kawo duk abin da ake bukata na kwalliya, amma ita kuma matar ba ta yi, to sai ka ga ya fi bukatar zama a waje fiy da cikin gidansa domin sai matarsa ta daina birge shi, da ganan sai yawan fada, sai kuma rabuwa wanda wannan laifin matane.

– Abinci: Da yawa daga cikin mata ba a koya masu girki a gidajensu wanda sai sun yi aure sannan abun ya zamar masu matsala, rashin iya girki babbar matsalace a zaman aure wanda za ka samu cewa duk abin da mace ta dafa babu dadi ko kuma ba a iya ci, shi kuma mai gidan yana
kawo duk abin da ake bukata wajen girki amma babu biyan bukata wajen girki wanda daga karshe idan ya gaji sai ka ga ya saka ta wanda wannan matsalar mace ce.

– Iya Magana : Wasu matan ba su san yanda za su yi magana da mijinsu ba, sai ka samu cewa ga matar da matukar kyau amma mijin baya gani saboda rashin iya magana, sai ya je waje ya biye wa wanda ba ta kai matarsa komai ba, amma ta iya magana, sai ta dauki hankalinsa wanda daga karshe zai ji ya gaji da ita wannan matar tashi kuma sai ya sake ta ya kawo wata.
-Tsafta: Tsafta tana daga cikin abin da zai sa mijinki ya soki, kamar tsaftar mahalli da kuma yara, namiji yana son ya ga ko da yaushe gidansa da kuma ya ransa da tsafta, amma wannan ya yi wahala a matan hausa, wanda rashin tsafta zai sa ya gaji da ita.

-Rashin Godiya: Wasu matan ba su da godiyar a kan irin kokarin da mijinsu yake masu, kullum yana bakin kokarinsa amma ba sa gani, wannan kuma yana kawo matsala daga karshe ka ga an rabu saboda ya gaji.
– Rashin Kula Da Dukiyar Miji: Dukiyar miji tana da matukar mahimmanci komin kankantar ta, amma da yawa daga cikin mata ba sa gani, sai subar dukiyar mijinsu ta lalace suna gani wanda shi kuma mijin bayan jin dadin haka, idan ya yi iya kokarinshi ba ta daina ba karshe sai ya sake ta.

– Gasa: Wasu matan suna da gasar cewa duk abin da aka yi wa wata mace suma sai an yi masu ba tare da kulawa da cewa mazajensu ba karfinsu daya ba, za ta matsama mijinta sai ya yi mata duk irin abin da ta gani a wajen wata macen wanda idan ya gaji ko kuma ba shi da hali, to sai dai su rabu da ita.

– Daukar Shawarwarin Banza: Wata macen ba ta da matsala da mijinta

amma tana daukar shawarar banza daga ‘yan’uwa da abokai, su kan ba ta shawarar banza a kan abin da za ta yi wa mijinta ta cutar da shi ko kuma ta hanyar sanya shi abin da baya iyawa wanda idan dai bai yi suba sai dai ya sake ta.

– Wulakanci Mata: Mata da yawa su kan so su ringa wulakanta mutanen da suka shafi bangaren mijinsu, kamar iyayenshi, yan’uwanshi da kuma
abokan arzikinshi, domin damar da ta samu ta zama matar dansu, dan’uwansu ko abokinsu wanda wasu mazan ba sa yarda da wannan to idan har macen ba ta daina ba to sai saki.

 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top