Tambaya:

Assalamu alaikumu. Da fatan Malam yana lafiya, shin Shaidan yana cikin jinsin Aljanune Ko Mala’iku kuma da me Allah ya halicci Mala’iku?

Amsa:

To dan’uwa malaman tafsiri sun yi sabani game da haka zuwa maganganu guda biyu :

1. Shaidan yana daga cikin mala’iku, saboda fadin Allah a cikin suratul Bakara aya ta:34, “Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala’iku su yiwa Annabi Adamu sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa da ya yi girman kai” togace Iblisa daga cikin wadanda ba su yi sujjada ba, yana nuna cewa yana daga cikin mala’iku.

2. Shaidan Aljani ne, saboda fadin Allah madaukakin sarki “ Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala’iku su yiwa Annabi Adamu sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa, wanda ya kasance daga cikin Aljanu” Kahaf aya ta : 50, sai ayar ta bayyana cewa daga aljanu yake.

Zance mafi inganci shi ne shaidan aljani ne, saboda an halicce shi ne daga wuta, su kuwa mala’iku an halicce su ne daga haske, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta : (2996) yake nuni zuwa hakan, sannan Shaidan yana da zuriyya, wacce take hayayyafa, mala’iku kuma ba sa haihuwa, wannan sai ya nuna ba daga cikinsu yake ba, Wannan yasa za’a dauki ayar suratul Bakara a matsayin tana nufin yana daga cikinsu ta fuskar zaman tare, amma ba ta fuskar halitta ba, sannan mala’iku ba sa sabawa Allah, shi kuma Iblisa yana sabawa Allah.

Allah ne mafi sani
Don neman Karin bayani duba : Tafsirin Ibnu-jarir 1 / 507 da Jami’u lada’if attafsir 1/278.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top