Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne ganin yadda goyon bayan da shugaban kasar ke samu a jihar yake samun koma-baya da kuma suka, saboda irin zarge-zarge na aikata ba daidai ba da suka faru a zaben, wanda a bayansa ne aka bayyana gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara.
Tuni dai jam'iyyar PDP wadda ta zo ta biyu a yawan kuri'u na zaben gwamnan ta yi watsi da sakamakon, kuma ta yi barazanar zuwa kotu, bisa abin da ta kira tayar da hankali, da kuma hana mutane kada kuri'a a lokacin zaben.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar da ta rubuta wannan koke, Alwan Hassan ya yi wa BBC karin bayani, da cewa:
''Mu abin da muke son uwar jam'iyya ta yi shi ne, a yi bincike a kan zaben cike-gibi da aka yi, a gano cewar; wanene ya shigo da mutane da suka hana mutane zabe, suka rubuta sakamako?
Duk wanda aka kama da wannan magana jam'iyya ta hukunta shi, hukuncin korarsa daga jam'iyya.''
Alwan Hassan ya ce suna da cikakkun shedu na irin badakalar da wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar tasu suka yi a lokacin zaben, har ta kai ga samun nasara.
Dangane da maganar cewa, me ya sa a lokacin da ake magudin ba su dauki mataki ba, sai ya ce, ai su ba 'yan sanda ba ne.
Saboda haka duk abin da za su yi, kawai shi ne sai dai su rubuta wa jam'iyya domin ta dauki mataki.
Kungiyar ta ce, tun lokacin da aka yi abubuwan da aka yi, ta ga ya dace ta zauna ta fitar da matsaya cewa, ita ba ta tare da abin da take cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar ganduje ya yi, saboda ya kayar da APC a Kano, kamar yadda 'yan wannan bangare na jam'iyyar suka ce.
'Yan kungiyar suka ce duk mutum mai hankali duk siyasarsa ba zai taba son abin da aka yi a kano ba, domin abin ya ma janyo wa shugaban kasar zagi.
Masu koken suka ce shugaban ya ki yin magana ne a kan lamarin saboda gudun kada a zarge shi da goyon bayan wani bangare.
A dalilin haka, ya zuba ido ga rundunar 'yan sanda da hukumar zabe ta kasar a kan su yi abin da ya kamata kan lamarin.
Kuma kungiyar ta ce shugaban bai ji dadin abin da ya faru a jihar ba kamar yanda Alwan Hassan ya ce:
''Wallahi Tallahi, Baba Buhari bai ji dadin abin da ya faru a Kano ba, kuma ba ya tare da abin da ya faru a Kano. Babu ruwan shugaban kasa a wannan harkar.''
'Yan wannan kungiya sun kuma kawar da zargin cewa wai ko suna yi wa jam'iyyar tasu ta APC zagon-kasa ne.
Suka ce, Shugaba Buhari shi ne jagora a jam'iyyar kuma tun da farko ya ce, su je su zabi dan takarar gwamna a kowace jiha, wanda suka san zai yi abu na adalci.
A dangane da fargabar jam'iyyarsu ta iya rasa kujerar gwamnan jihar Kanon idan aka yi bincike, Mallam Alwan ya ce: ''Duk abin da talaka ya zaba ya ce a ba shi, a ba shi. Me ya sa?
Bauchi mutuwa suka yi da gwamnonin da suka fadi, Adamawa yanzu ya mutu?''
Mallam Alwan ya ce babu wata maganar ko sun hada baki da 'yan hamayya ne ya sa suke bayyana wannan matsayi.
Ya yi nuni da hotunan bidiyo da ya ce duniya ta gani, wadanda a ciki aka ga mataimakin gwamnan jihar ta kano da Kwamishinan kananan hukumomi, wadanda ya ce sun fi kusa da gwamna, sun je karfe biyun dare sun yaga sakamakon zabe.
©HausaLoaded
Post a Comment