Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni ya amince da kafa yan sandan jiha da na karamar hukuma.
Ya kuma amince da korar jami’an yan sanda 37 kamar yadda kwamitin shugaban kasa na kare hukumar kare hakkin hukumar akan sabonta SARS ta bayar da shawara.
Kwamitin a cewar Ojukwu ta samu korafe-korafe 113 kan zargin take hakkin dan adam daga fadin kasar da kuma yarjejeniya 22 kan yadda za a sake fasalin SARS da rundunar yan sandan Najeriya baki daya.
Wasu daga cikin shawarwarin hada sun da, “muhimmin kokari wajen tanadar da kudade da kayan aiki ga rundunar yan sandan Najeriya; karfafa fasahar labarai da sadarwa na rundunan; kafa rundunar yan sanda na jiha da karamar hukuma.”
A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa a yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon babban zaben kasa na 2019, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gano wani bakin tuggu da fadar shugaban kasa ke kullawa domin cin galaba a kansa a gaban kotun daukaka kara.
Atiku da kungiyar sa ta kwararrun lauyoyi na ci gaba da zargin fadar shugaban kasa da kawo jinkirin fara sauraron karar sa ta kalubalantar sakamakon zaben kasa domin cimma manufa ta watsi da karar sa.
©HausaLoaded
Post a Comment