.
Kafin yanzu muna kallon mace mai bin maza ita
tafi kowace mace lalacewa a duniya... Amma a
halin da ake ciki yanzu mun zo wani zamani
wandaa wurin 'yan mata shaye shaye da
mad'igo shine wayewa...

Tun suna yin abinsu a boye har abin ya fito fili
domin idan yarinya tana irin wannan harkar zaka
ga kowa ya sani har misali ake yi da ita ana
nunata a unguwa... Munin wannan harkar ta sa
'yan mata yanzu ba su da kunya kuma sun daina
mu'amula da maza sai dai su dinga kula mata
'yan uwansu...

A shekaru da dama da suka wuce ana danganta
'yan mata masu harkar mad'igo sun dauko
wannan dabi'ar daga boarding school ne... To
amma yanzu abin da zai baka mamaki 'yan mata
masu matsakaicin shekaru wadanda suke karatun
boko da islamiya gaban iyayensu zaka ji labarin a
cikin gari cewa tana daga cikin masu irin wannan
dabi'ar...

Iyaye da shuwagabanni sun kasa mayar da
hankulansu domin a shawo kan wannan matsalar
wacce ta zama ruwan dare gama duniya... An sa
ido tarbiyyar 'ya 'ya mata sai qara lalacewa take
yi fiye da tunanin mai tunani wai har lalacewar ta
kai ana kunnen doki tsakanin 'yan mata da
samari wurin mummunan dabi'u...

Idan har da gaske ana so a shawo kan wannan
matsalar to fa dole sai an bi wadannan hanyoyin
sannan :-

- Dole iyaye su sa ido akan su waye qawayen'
yar su... Matuqar basu gamsu da wadannan
qawayen ba to su gimtse wannan alaqar...

- Handset, musamman Android domin ita ce
babbar hanya mafi saurin lalata tarbiya... Da
waya za'a hurewa yarinya kunne kuma da ita
za'a kirata ta je kuma da waya ce za'a fara turo
mata wasu picts ko video masu nuna tsiraici har
sha'awarta ta motsa... Saboda haka yakamata a
daina barin 'yan mata suna rike waya... Idan
kuma rike wayar ya zama dole to a bata qarama
wacce zata amsa kira kawai...

- Fita ba bisa qa'ida ba... Kullum iyaye suna kallo
yarinya zata dauki hijabi ta fita akan wani dalili
wanda bai zama dole sai ta fita din ba... Idan ta
fita shikenan duk inda ta ga dama zata leqa
kuma sai lokacin da ta ga dama zata dawo...

- Yarinya ta shigo da babbar kyauta da sunan
qawa ko saurayi ya bata... Lallai a dakatar da
yarinyar daga amsar irin babbar kyauta daga
hannun ko waye...

Lallai yakamata iyaye su saka idanu kuma su
kula da kiwon da Allah ya basu akan 'ya'yansu
domin wallahi rashin sa' ido da rashin bibiyar
halin da 'ya' yanmu ke ciki ya sa 'yan matan ga
halaka...

Jiya wani yana bani labari yace wallahi akwai
hotel din da mata ke kamawa mata 'yan uwansu
d'aki... Daga baya da masu hotel din suka lura
sai suka sa dokar hana mata d'aki... Yanzu cewa
yayi matan da suka fahimci haka sai su kira
namiji su bashi kudi ya tafi ya kama musu d'aki
su bashi ladanshi... Yace kuma ba wai 'yan mata
kawai ba yace har da matan aure da zawarawa...

Haka dai wani yana bani labarin yace jiya jiyan
nan wata ke bashi labarin cewa qawarsu wata
tayi mata sayayya tafi ta dubu d'ari ciki har da
sutura kala 12... To wallahi idan zamu farka mu
farka domin wannan al'amari qara gaba yake yi...
Zaka ga yarinya mai nutsuwa da tarbiya bata
kula samari amma daga baya ta fada tarkon
wadannan mutanen ta hanyar jan hankalinta da
abin duniya...

Wasu 'yan matan kuma sharri ake musu dan
kawai a bata musu suna ko kuma dan suna
qawance da wacce take yi ko ake zargi...

Lallai mata ku kula domin watarana ku iyaye ne
kuma ku ne makarantar farko... Ya kenan
tarbiyyar 'ya'yanki zai kasance idan aka ce kina
da irin wadannan mutanen dabi'un???

YA ALLAH KA KAREMU KA KARE ZURI'ARMU
DAGA AIKATA DUK WANI AIKIN ASHSHA...




✍📚ISLAM FOR ALL MUSLIM FOUNDATION📓


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top